Yanzu Yanzu: Mutanen Abuja sun cika da tsoro yayinda yan Shi’a dake zanga-zanga ke ci gaba da karawa da yan sanda

Yanzu Yanzu: Mutanen Abuja sun cika da tsoro yayinda yan Shi’a dake zanga-zanga ke ci gaba da karawa da yan sanda

Mazauna Abuja sun cika da tsoro yayinda jami’an yan sanda ke karawa day an Shi’a a babban birnin tarayyan Najeriya.

Zuwa yanzu dai babu cikakken rahoto kan lamarin sai dai mazauna yankin sun rahoto cewa motocin yan sanda na ta kora masu zanga-zangan dake jifarsu da duwatsu da sauran abubuwa.

Mafi akasarin rikicin na faruwa ne a kusa da kasuwar Wuse na babban birnin.

Yanzu Yanzu: Mutanen Abuja sun cika da tsoro yayinda yan Shi’a dake zanga-zanga ke ci gaba da karawa da yan sanda

Yanzu Yanzu: Mutanen Abuja sun cika da tsoro yayinda yan Shi’a dake zanga-zanga ke ci gaba da karawa da yan sanda

Sai dai masu ciniki a kasuwar sunce akwai kwanciyar hankali a cikin kasuwar.

KU KARANTA KUMA: Nyass ba Allah ba ne, masu danganta shi da Allah sun kafirta - Inji Sheikh Sani Yahaya Jingir

Majiyarmu ta bayyana cewa ana ta amfani da barkonon tsohuwa wajen kora masu zanga-zangan dake haddasa tsoro a tsakanin masu wucewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel