Zaben 2019: Watakila Atiku, Saraki da Tambuwal suyi takara da Buhari a Jam’iyyar SDP

Zaben 2019: Watakila Atiku, Saraki da Tambuwal suyi takara da Buhari a Jam’iyyar SDP

- Ana cigaba da hada karfi wuri guda domin tunkarar zaben 2019

- Jam'iyyun adawa na laluben hanyar da zasu bi don ganin sun kori Buhari gada Villa

- Wasu 'yan cikin APC da na PDP na neman hanyoyin da za su sami tikitin tsayawa takara domin kayar da Buhari

Shugaban Jam’iyyar SDP na riko a jihar Anambra Chief Vincent Obi ya bayyanawa manema labarai a garin Awka dake jihar Anambra cewa, kimanin Mutane 7 ne suka nuna sha’awarsu ta neman sahalewa don su yiwa Jam’iyyar SDP takara a zaben 2019.

Zaben 2019: Watakil Atiku, Saraki da Tambuwal suyi takara da Buhari a Jam’iyyar SDP

Zaben 2019: Watakil Atiku, Saraki da Tambuwal suyi takara da Buhari a Jam’iyyar SDP

Vincent Obi ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da fara yin rijistar mambobinta a duk kananan hukumomi 21 na jihar.

A cewarsa Jam’iyyar ta dawo da karfin ta nedon karbar shugabancin kasar nan.

Chief Obi ya kuma sha alwashin kalubalantar Jam’iyya mai mulki ta APC da kuma babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP a dukkanin zabuka masu zuwa, domin kuwa Ja’iyyar na hasashen yiwa Mutane rijistar katin shaidar zama dan Jam’iyyar har Mutane Miliyan biyu kafin gudanar da zabe 2019.

KU KARANTA: Wata-sabuwa: Farfesa Osinbajo yayi barazanar yin murabus daga mukamin sa

Bisa wannan dalili ne shugaban yayi kira ga duk ‘yan Jam’iyyar da su bazama don mallakar nasu katin tare kuma jawo mutane su shigo Jam’iyyar tasu domin za’a fara rijista baji ba gani.

Daga nan ne Obi ya bayar da tabbacin cewa duk rububin da ake na takara a Jam’iyyar, su har yanzu basu fidda gwani ba, domin Jam’iyyar na da tsohon tarihi na jajircewa da hangen nesa.

Ya kuma shaida cewa daga cikin masu neman takarar har da shugaban Majalisar wakilai Sanata Dr. Bukola Saraki da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da tsohon kakakin Majalisar wakilai kuma Gwamnan jihar Sokoto Barrister Aminu Tambowel da tsohon shugaban Majalisar Dattijai Sanata David Mark da kuma Gwamnan jihar Gombe Dr. Ibrahim Dankwambo.

Tare da Sanatoci 60 da suke son yin takara a Jam’iyyar, amma ba tare da ya kama suna ba.

Sanann kara da cewa nan gaba kadan zasu gudanar da gangamin jam’iyyar domin zabar shuwagabanninta a matakai daban-daban bayan kammala rijistar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel