Zanga-zangan yan Shi’a: Sojoji, yan sanda, jami’an NSCDC sun mamaye birnin tarayya Abuja

Zanga-zangan yan Shi’a: Sojoji, yan sanda, jami’an NSCDC sun mamaye birnin tarayya Abuja

Jami’an soji, yan sandan, NSCDC sun mamaye unguwannin da ke wajen Transcorp Hiton bayan mumunar zanga-zangan da ya faru jiya Litinin, 16 ga watan Afrilu, 2018.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa yan kungiyar Shi’a sun gudanar da zanga-zanga kan cigaba da tsare shugabansu, Sheikh Ibrahim Zakzaky, duk da cewan kotu ta bada umurnin sakeshi.

Wani idon shaida, Bola Adeniran, ya bayyanawa manema labarai cewa rikicin ya fara ne sanadiyar hana yan shi’a shiga farfajiyar Unity Fountain inda suka saba gudanar da zanga-zanga.

Shelkwatar yan sandan babban birnin tarayya, a yau Litinin ta damke mambobin kungiyar Shi’a 115 a wani zanga-zanga da sukayi yau a Abuja.

Zanga-zangan yan Shi’a: Sojoji, yan sanda, jami’an NSCDC sun mamaye birnin tarayya Abuja

Zanga-zangan yan Shi’a: Sojoji, yan sanda, jami’an NSCDC sun mamaye birnin tarayya Abuja

Hukumar ta yi watsi da rahotannin cewa an yi rashin rayuka. Kakakin hukumar yan sanda, DSP Anjuguri Manzah, yace: “Babu rayuwar da aka rasa saboda jami’an yan sandan sunyi iyakan kokarin cikin kwarewa.”

KU KARANTA: Babu wanda aka kashe amma mun damke yan Shi’a 115 – Kakakin yan sanda

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa rikici ya barke tsakanin mambobin kungiyar Shi’a da jami’an yan sanda a farfajiyar Unity Fountain dake Abuja a yau. DSP Anjuguri Manzah ya yi jawabin cewa masu zanga-zangan sun raunata jami’an yan sanda 22 kuma sun bannatar da dukiyoyon gwamnati da motocin hukumar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel