Da dumi-dumi: An damke yar kunar bakin wake a Maiduguri

Da dumi-dumi: An damke yar kunar bakin wake a Maiduguri

Jami’an yan sanda jihar Borno a jiya Litinin sun damke wata yar kunar bakin wake kusa da sansanin yan gudun hijra da ke Bakassi, garin Maiduguri, jihar Borno.

Hukumar yan sandan ta saki jawabi a yau Talata inda suka ambaci sunan yarinyar a matsayin Zara Idris.

Jawabin da kakakin hukumar, Edet Okon, ya saki ya bayyana cewa an samu nasarar damketa ne kafin ta samu daman tayar da Bam din kusa da sansanin yan gudun hijran.

Yace: “Yayinda aka hangota, jami’an yan sanda suka farga suka tare hanya domin hanata samun dama shiga cikin gari."

Da dumi-dumi: An damke yar kunar bakin wake a Maiduguri

Da dumi-dumi: An damke yar kunar bakin wake a Maiduguri

Kwamishanan hukumar yan sandan jihar ya yi kira ga al’umman gari su cigaba da ayyukan gabansu ba tare da tsoro ba kuma kada su gajiya wajen jawo hankalin hukuma idan suka abinda basu yarda da shi ba.

Kwanakin nan, yan kunar bakin wake suna kai hare-haren Bam kauyukan da ke wajen Maiduguri.

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 6 da ya kamata duk dan bautar kasa ajin 'A' ya sani

A watan Maris, yan kunar bakin wake sun kai hari kauyen Muna Zawiya da ke karamar hukumar Mafa amma basu samu nasaran kashe kowa ba face kawunansu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel