Mun tsakuro muku: Muhimmman batutuwa 5 da shugaba Buhari ya tauna da Miss May ta Ingila

Mun tsakuro muku: Muhimmman batutuwa 5 da shugaba Buhari ya tauna da Miss May ta Ingila

- Shugaba Buhari a hutunsa ya tsaya gaisawa da shugabar Ingila May

- Sun tattauna batutuwa da dama, ciiki harda batun takararsa

- An zargi shugaban da kin yi wa kasa bayani, sai dai a jiyo batutuwan a wata kasa

Mun tsakuro muku: Muhimmman batutuwa 5 da shugaba Buhari ya tauna da Miss May ta Ingilla

Mun tsakuro muku: Muhimmman batutuwa 5 da shugaba Buhari ya tauna da Miss May ta Ingilla

A ziyarar sa ta Ingila, shugaba Buhari ya zanta da takwararsa ta Ingila, Theresa May, kan wasu muhimman batutuwa, musamman kan al'amuran cikin gida da suka shafi tsaro, tatttalin arziki, Boko Haramun, da ma batun Chibok.

1. Tsaro:

Kan tsaro, musamman batun Boko Haram da ma matan Chibok: Shugaba May a jawabinta tace Birtaniya zata cigaba da aiki da Najeriya a gurin horarwa da samar da makamai ga sojojin kasar domin yaki da ta'addanci.

Shugaban yace suma a nasu bangaren, suna iyakar kokarinsu na ganinn sun ceto 'yan matan.

2. Tattalin Arziki:

A fannin tattalin arziki: "Munyi yakin neman zabe ne da alkawura guda uku. Tsaron kasar, farfado da tattalin arziki da fada da rashawa" inji shugaban kasan.

"Muna da zabe shekara mai zuwa, hankalin 'yan siyasa ya karkata a can amma ni abinda yafi damuna shi ne tsaro da tattalin arziki"

Shugaban yayi jinjina ga kamfanonin Birtaniya kamar Unilever, Cadbury da sauransu. "wadanda suke tare da mu a kowanne hali. Har lokacin yakin Biafra basu guje mu ba"

"Muna bukatar kamfanonin birtaniya dasu zo Najeriya don karin hannayen jari. Muna godiya bisa ga gudummawar makamai da horar da sojojin mu da kuke yi don fada da ta'addanci, amma muna so a cigaba da cinkayya da saka hannayen jari. "

3. Sauyin Yanayi:

Batun sauyi Yanayin duniya ma ya sami la'akari: Shugaban Buhari yace dole ne a samarda hanyar da kogin Congo zai dinga ba tafkin Chadi ruwa.

Kamar yanda yace "Tafkin dai a halin da ake ciki bai wuce kaso goma cikin dari ba na ruwan da aka sanshi da shi. Idan kuwa aka samu tafkin ya cika, sama da mutane miliyan 40 a Najeriya, Nijar, kamaru, Chadi da wasu kasashen zasu amfana.

Idan aka cika tafkin Chadi, zai rage yawan samarinmu da ke zuwa turai domin kara musu matsaloli. Mun dawo da mutane 4,000 daga Libya kwanannan masu shekaru kasa da 30, kuma ba a Libya kadai suka tsaya ba, turai suka nufa".

DUBA WANNAN: Kasashen da aka haramtawa 'yann Saudiyya zuwa

4. Zabukan 2019:

Da yazo kan batun zabuka kuwa, shugaban yace shi ba wannan ya sanya a gaba ba, watau tazarcen 2019, yace shi alkawurran da ya daukarwa mutane kafin zabe, musamman tsaro da tattalin arziki su ya sanya gaba.

5. Noma da ilimi:

Shugaban yayi tsokaci ga Shugaba May akan cigaban da aka samu ta bangaren noma.

"Ina farincikin nasarorin da muka samu a noma. Mun rage shigo da shinkafa kusan kashi 90 cikin dari, mun adana da yawa don cinkayya tsakaninmu da wasu kasashe,kuma mun samar da aikin yi. Muna samun cigaba sosai ta fannin abinci"

A bangaren ilimi, shugaba Buhari yace an kara maida hankali akan ilimi saboda "A wannan lokacin na kimiyya da fasaha mutum mai ilimi zai iya dogaro da kanshi. Ilimi na da matukar amfani. Muna bukatar kwararrun malamai da makarantu masu isassun kayan aiki domin cigaban yara masu tasowa"

Tsokacin masu adawa:

Sai dai, ana yawan zunden shugaban da cewa baya yi wa 'yan kasa gamsasshen bayani, ko ma sakin bayanai akan wasu batutuwan, sai dai kawai in yaje wata kasa a jiyo shi yana zuba, ko ta hannun wasu 'yan jaridar na can haka.

Shugaba Buhari kuma zai nufi Amurka don ganawa ta musamman da takwaransa Donald Trump na Amurkar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel