Dalilin da yasa nake takarar gwamna a Kano – Zaura

Dalilin da yasa nake takarar gwamna a Kano – Zaura

Wani dan kasuwa sannan dan siyasa daga jihar Kano, Alhaji Abdulsalami Abdulkarim Zaura, ya bi sahun masu takarar kujerar gwamna a jihar.

Zaura yace ya amsa kiraye-kirayen da mutanen jihar Kano keyi masa ne na ya yi takarar gwamna a jihar.

Da yake Magana a Abuja, yace ya shirya tsaf domin ganin ya cika burin mutanensa a karkashin jam’iyyar Green Party of Nigeria (GPN).

Ya kara da cewa yanke shawararsa na neman kujerar gwamna a jihar ya kasance rokon matasa a jihar.

Dalilin da yasa nake takarar gwamna a Kano – Zaura

Dalilin da yasa nake takarar gwamna a Kano – Zaura

Ya ce babban burinsa shine dawo da martabar jihar a matsayinta na cibiyar ciniki.

KU KARANTA KUMA: Tsohon dan Firamare yayi shekara hudu yana yiwa aikin Likitanci sojan gona

A cewarsa, Kano na fuskantar koma baya a lokaci guda. “Abun bakin ciki ne ganin jiha mai inganci kamar Kano tana fuskantar kalubale ciki harda koma bayan tattalin arziki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel