Kotu tayi watsi da bukatar tsohon gwamnan jihar Niger na tafiya Umrah

Kotu tayi watsi da bukatar tsohon gwamnan jihar Niger na tafiya Umrah

Wata babban kotun tarayya dake garin Minna, babban birnin jihar Niger ta yi watsi da rokon tsohon gwamnan jihar Niger, Dr Muazu Babangida Aliyu, na sakin fasfot dinsa domin ya samu damar tafiya aikin Umrah.

Babangida Aliyu da Umar Muhammad Nasko, tsohon kwamishinan muhalli, na fuskantar shari’a na wasu tuhume-tuhume takwas da ake masu inda aka zarge su da zambar kudi kimanin naira biliyan biyu.

Kotu tayi watsi da bukatar tsohon gwamnan jihar Niger na tafiya Umrah

Kotu tayi watsi da bukatar tsohon gwamnan jihar Niger na tafiya Umrah

Tsohon gwamnan ya dawo sauraran kararsa da hukumar EFCC ta shigar a ranar Laraba da ta gabata inda ya gabatar da wata takarta na rokon kotu ta bashi damar tafiya aikin Umrah.

KU KARANTA KUMA: Tsohon dan Firamare yayi shekara hudu yana yiwa aikin Likitanci sojan gona

Sai dai mai shari’a Yellim Bogoro yace lallai dole tsohon gwamnan ya dunga gabatar da kansa a gaban shari’a koda yaushe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel