Tatallin arziki: Firayim Ministar Birtaniya ta jinjinawa Shugaba Buhari

Tatallin arziki: Firayim Ministar Birtaniya ta jinjinawa Shugaba Buhari

- Theresa May tace in ana maganar tattalin arziki Buhari yayi abin a yaba

- May ta jaddada abin da Bill Gates ya fadawa Gwamnatin kasar kwanaki

- Ingila tace za ta cigaba da taimakawa Najeriya wajen yaki da ta’addanci

Firayim Ministar kasar Birtaniyya watau Theresa May ta ce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi abin a yaba a game da sha’anin tattalin arziki wanda yana cikin alkawuran da yayi daga hawan sa mulki kawo yanzu.

Tatallin arziki: Firayim Ministar Birtaniya ta jinjinawa Shugaba Buhari

Firayim Ministar Kasar Ingila ta gana da Shugaba Buhari

A jiya ne Shugaban kasa Buhari ya gana da Shugabar ta Birtaniya a gidan ta da ke Landan. Theresa May tace dole a yabawa kokarin da Shugaba Buhari yayi na cika alkwarin da ya dauka game da tattalin arzikin Najeriya.

KU KARANTA: Wayyo Allah: An goga mani bakin jini a kasar nan Inji IBB

May tace amma fa duk da haka sai Shugaban kasar ya dage wajen ganin an cigaba da samun habakar tattali. Bayan nan kuma Firayim Ministar ta bayyana cewa sai Gwamnatin Buhari ta kara dagewa wajen harkar ilmi.

Theresa May ta kuma ce Ingila za ta cigaba da marawa Najeriya baya musamman wjaen yaki da ta’addanci. Kwanakin baya dai Mai kudin Duniya Bill Gates ya nemi Najeriya ta kara dagewa kan sha’anin ilmi da kiwon lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel