SwissGolden: EFCC ta waigi masu damfarar mutane, ta ceto N216m

SwissGolden: EFCC ta waigi masu damfarar mutane, ta ceto N216m

- Hukumar yaki da almundahana ta kudi ta kwato Naira miliyan 216 daga yan'damfara "Swiss Golden"

- Hukumar yaki da almundahana ta kudi ta samo N216,402,565.05 daga Swiss Golden, wani kamfanin hannun jari na siye da siyarwar zinare a yanar gizo

- Karbo kudin dai ya biyo bayan korafe korafen da hukumar ta samu ne daga dumbin mutanen da suka zuba hannayen jari kuma kamfanin suka ki biyansu riba ko uwar kudin

SwissGolden: ECC ta waigi masu damfarar mutane, ta ceto N216m

SwissGolden: ECC ta waigi masu damfarar mutane, ta ceto N216m

Hukumar yaki da almundahana ta kudi ta kwato Naira miliyan 216 daga 'yan damfara a "Swiss Golden".

Hukumar yaki da almundahana ta kudi ta samo N216,402,565.05 daga Swiss Golden, wani kamfanin hannun jari na siye da siyarwar zinare a yanar gizo.

Karbo kudin dai ya biyo bayan korafe korafen da hukumar ta samu ne daga dumbin mutanen da suka zuba hannayen jari kuma kamfanin suka ki biyansu riba ko uwar kudin.

Bayan karbar korafin, hukumar ta kira wadanda ake kara, Maxim Lobaty, Dan kasar Rasha da mutane biyu 'yan kasar Najeriya Austin Emenike da Dickson Nonso Onuchukwu a Legas.

An kaisu ofishin hukumar da ke kano domin karin bincike. Swiss Golden wacce take da hedkwata a Hong Kong an gano cewa cibiyace ta damfarar mutane kudaden su.

DUBA WANNAN: Yadda aka kashe Zainab da diyarta a Legas

Bayan tsananin bincike a ofishin hukumar ta kano, Maxim da sauran wadanda ake tuhuma suka mika Naira miliyan dari biyu da sha shida, da dubu dari hudu da biyu, da dari biyar da sittin da biyar ga hukumar.

A lokacin binciken an gano cewa kamfanin Swiss Golden sun damfari sama da 'yan Najeriya dubu bakwai sama da Naira biliyan 3.

Har yanzu ana cigaba da bincike kuma ana kokarin ganin an samo duka kudin tare da gurfanar da wadanda ake zargi gaban shari'a.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel