Jami’an Sojin Najeriya sunyi arangama da ‘yan ta’addan makiyaya a jihar Binuwai

Jami’an Sojin Najeriya sunyi arangama da ‘yan ta’addan makiyaya a jihar Binuwai

- Sojin 72 Bataliyar Special Force lokacin da take gudanar da aikin Operation MESA a jihar Binuwai tayi arangama da ‘yan ta’addan Makiyaya 20

- Sojin sunyi nasarar kashe hudu daga cikin Makiyayan sai sauran kuma sunyi nasarar tserewa da raunuka a jikinsu na harbin bindidiga

- Sojin sunyi nasarar karbe bindigogi hudu kirar AK-47, sai harsashi 7.62mm guda biyar sai kuma harsashi 28 mai girman 7.62 irin jami’an ‘Yan Sanda

Sojin 72 Bataliyar Special Force lokacin da take gudanar da aikin Operation MESA tayi arangama da ‘yan ta’addan Makiyaya 20, a Yogbo dake karamar hukumar Guma, dake jihar Binuwai.

Sojin sunyi nasarar kashe hudu daga cikin Makiyayan sai sauran kuma sunyi nasarar tserewa da raunuka a jikinsu sakamakon harbin bindidiga.

Jami’an Sojin Najeriya sunyi arangama da ‘yan ta’addan makiyaya a jihar Binuwai

Jami’an Sojin Najeriya sunyi arangama da ‘yan ta’addan makiyaya a jihar Binuwai

Sojin sunyi nasarar karbe bindigogi hudu kirar AK-47, sai harsashi 7.62mm guda biyar sai kuma harsashi 28 mai girman 7.62 irin jami’an ‘Yan Sanda.

KU KARANTA KUMA: Tsohon dan Firamare yayi shekara hudu yana yiwa aikin Likitanci sojan gona

Brigedier Janar Texas Chukwu Daraktan hukumar mai kula da harkoki da jama’a yace, hukumar Sojin tana sanarda al’umma cewa tana kan kokarin magance ta’addanci da kuma ‘yan ta’adda a fadin kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel