Shahada: Zaftarewar kasa ta kashe mutum 2, jikkata 3 a Arewa

Shahada: Zaftarewar kasa ta kashe mutum 2, jikkata 3 a Arewa

Labarin da muke samu daga majiyar mu na tabbatar mana da cewa zaftarewar kasa tayi sanadiyyar mutuwar akalla mutane biyu da suka hada da Mati Bako mai shekaru 17 da kuma Tanimu Kwalle mai shekaru 25 a karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa.

Kamar yadda muka samu, mai magana da yawun 'yan sandan Najeriya a jihar SP Abdu Jinjiri ne ya tabbatar da afkuwar hakan ga manema labarai na Najeriya.

Shahada: Zaftarewar kasa ta kashe mutum 2, jikkata 3 a Arewa

Shahada: Zaftarewar kasa ta kashe mutum 2, jikkata 3 a Arewa

KU KARANTA: An goga mun bakin jini a kasar nan - IBB

Legit.ng ta samu haka zalika cewa SP Abdu Jinjiri ya kuma kara da cewa kasar ta rufta da matasan ne a yayin da suke hakar rami a wani kauyen karamar hukumar da ake kira Barima.

A wani labarin kuma, Babban jami'in hukumar agajin gaggawa ta gwamnatin tarayya dake kula da shiyyar Arewa maso gabas mai suna Bashir Garga ya bayyana cewa kawo yanzu dai kimanin 'yan gudun hijira dubu takwas ne hukumar su ta maida gidaddajin su a karamar hukumar Bama.

Bashir yayi wannan ikirarin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda kuma ya bayyana cewa dukkan wannan nasarar da suka samu na daga kyakkyawan shugabancin shugaba Muhammadu Buhari.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel