Jam'iyyar PDP ta jajantawa 'yan shi'a game da arangamar su da sojoji a Abuja

Jam'iyyar PDP ta jajantawa 'yan shi'a game da arangamar su da sojoji a Abuja

Babbar jam'iyyar ta Peoples Democratic Party (PDP) a wata sanarwar da ta fitar ta jajantawa dukkanin daukacin mabiya shi'a almajiran Zakzaky musamman ma wadanda suka yi arangama da 'yan sandan tarayyar Najeriya yau a filin 'Unity Fountain' na garin Abuja.

Jam'iyyar wadda ta bayyana matukar jajenta, ta kuma yi Allah-wadai game da yadda suka ce gwamnatin ta tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ke cigaba da tsare shugaban mabiya mazhabar shi'ar duk kuwa da umurnin kotu a kan hakan.

Jam'iyyar PDP ta jajantawa 'yan shi'a game da arangamar su da sojoji a Abuja

Jam'iyyar PDP ta jajantawa 'yan shi'a game da arangamar su da sojoji a Abuja

KU KARANTA: Karin haske game da daukar aikin sojoji a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa 'yan shi'a dai sun samu arangama da 'yan sandan Najeriya da ranar yau inda aka tarwatsa su suna cikin gudanar da zanga-zangar lumana ta neman gwamnatin tarayya ta sako masu jagoran su.

A wani labarin kuma, Yan majalisar dattijan nan masu goyon bayan muradun shugaban kasa Muhammadu Buhari da suka hada wata 'yar kwarya-kwaryar kungiya mai suna Parliamentary Support Group (PSG) ta yi tir da korar da akayi wa daya daga cikin mambobin ta daga zauren.

Haka ma kuma 'yan majalisun dattijan da ke a kungiyar sun bayyana cewa shugaban majalisar Dakta Bukola Saraki bai isa ya cire masu son shugaba Buhari ba duk irin tuggun da zai jagoranci kulla masu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel