Sabbin bayanai sun kara bankado wadanda suka ci kudin makamai daga hannin Dasuki

Sabbin bayanai sun kara bankado wadanda suka ci kudin makamai daga hannin Dasuki

Sabbin bayanai da ke fitowa daga hannun hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta bayyana cewa shugaban jam'iyyar PDP Mista Prince Uche Secondus ya karbi Naira miliyan 250 daga hannaun Dasuki domin gudanar da wasu ayyuka na musamman.

Wannan dai kamar yadda muka samu na kunshe ne a cikin wani rahoton da hukumar ta kammala wanda kuma wakilin majiyar mu ya gani wanda aka kuma bayyana cewa ya anshi kudaden ne a gabanin gudanar da zabukan 2015.

Sabbin bayanai sun kara bankado wadanda suka ci kudin makamai daga hannin Dasuki

Sabbin bayanai sun kara bankado wadanda suka ci kudin makamai daga hannin Dasuki
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun samu galaba kan yan Boko Haram

Legit.ng ta samu har wayau cewa kudaden an ce shi ya karbi Naira miliyan 50 da kansa yayin da kuma ya karbi Naira miliyan 200 ta hannun wani dan aike da ya tura.

A wani labari kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya Ibrahim Babangida ya ayyana cewa shi yasan babu wani dan Najeriyar da zi dauki maganganun shi da muhimmanci musamman ma idan ya rubuta su saboda bakin fentin da yace an shafa mashi.

Janar Babangida dai yayi wannan bayanin ne a lokacin da ake fira da shi a gidan Talabijin din Channels inda aka tambaye shi ko zai rubuta tarihin sa a nan gaba musamman ma saboda ya fayyace wa jama'a babban dalilin da ya sa ya soke zaben 12 ga watan Yuni.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel