Mutanen da za su iya maye gurbin Shugaba Buhari daga Arewacin Najeriya

Mutanen da za su iya maye gurbin Shugaba Buhari daga Arewacin Najeriya

Kwanakin baya Fasto Tunde Bakare ya bayyana cewa daga Arewacin Najeriya za a samu wani da kwatsam zai buge Shugaba Muhammadu Buhari. Tun daga nan 'Yan jarida su ka shiga laluben ko wanene wannan 'Dan takara.

Mun dai kawo jerin wadanda ake tunani za su fi zama barazana ga Shugaban kasar ta fuskar siyasa.

Mutanen da za su iya maye gurbin Shugaba Buhari daga Arewacin Najeriya

Sule Lamido na PDP na iya kawowa Shugaba Buhari cikas

1. Rabiu Kwankwaso

Cikin 'yan kwanakin nan jama'a sun kara ganin yadda tsohon Gwamnan na Kano yake da farin jini matuka. Ba mamaki idan Sanata Kwankwaso ya nemi ya ja da Shugaban kasa Buhari.

KU KARANTA: Watakila Tinubu yayi wa Osinbajo ritaya kwanan nan

2. Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jigawa watau Sule Lamido ya saba sukar Jam'iyyar APC da Gwamnatin Buhari. Ba shakka Lamido yana da dinbin mabiya a Jam'iyyar PDP har a wajen Arewacin Najeriya.

3. Aminu Tambuwal

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri yana cikin wadanda ake ganin za su iya neman takarar Shugaban kasa. Akwai manyan 'Yan siyasa da ke bayan Tambuwal har da Jam'iyyun adawa.

Sai dai bayan wadannan akwai irin su Malam Ibrahim Shekarau, Atiku Abubakar, da Ibrahim Dankwambo da ka iya neman takara a 2019 amma da wuya idan har da su Fasto Bakare ya ke magana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel