Babu wanda aka kashe amma mun damke yan Shi’a 115 – Kakakin yan sanda

Babu wanda aka kashe amma mun damke yan Shi’a 115 – Kakakin yan sanda

Shelkwatar yan sandan babban birnin tarayya, a yau Litinin ta damke mambobin kungiyar Shi’a 115 a wani zanga-zanga da sukayi yau a Abuja.

Hukumar ta yi watsi da rahotannin cewa an yi rashin rayuka.

Kakakin hukumar yan sanda, DSP Anjuguri Manzah, yace: “Babu rayuwar da aka rasa saboda jami’an yan sandan sunyi iyakan kokarin cikin kwarewa.”

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa rikici ya barke tsakanin mambobin kungiyar Shi’a da jami’an yan sanda a farfajiyar Unity Fountain dake Abuja a yau.

DSP Anjuguri Manzah ya yi jawabin cewa masu zanga-zangan sun raunata jami’an yan sanda 22 kuma sun bannatar da dukiyoyon gwamnati da motocin hukumar.

Babu wanda aka kashe amma mun damke yan Shi’a 115 – Kakakin yan sanda

Babu wanda aka kashe amma mun damke yan Shi’a 115 – Kakakin yan sanda

Kana masu zanga-zangan sun kai raunata mutanen gari, sun hana yan kasuwa sukuni kuma sun fasa motocin jama’a.

Yace hukumar yan sandan sun kaddamar da bincike cikin al’amarin. Ya kara da cewa za’a gurfanar da su a kotu muddin aka kaddamar da bincike.

KU KARANTA: Uche Secondus, shugabannin PDP sunyi ganawar sirri da IBB

Hukumar yan sanda ta gargadi mambobin kungiyar Shi’a kan tayar da zaune tsaye a birnin tarayya Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel