Da dumi-dumi: Uche Secondus, IBB sunyi ganawar sirri

Da dumi-dumi: Uche Secondus, IBB sunyi ganawar sirri

Shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Prince Uche Secondus, tare da mambobin ja’iyyar sun shiga ganawar sirri da tsohon shugaban kasan Najeriya Janar Ibrahim Babangida a Minna.

Mambobin sun isa garin Minna ne a jirgin Shata inda suka karasa fadar Babangida.

Sunyi ganawar sirrin ne tare da shugabannin jam’iyyar PDP na jihar Neja karkashin jagorancin Barrister Tanko Beji.

Daya daga cikin jigogin jam’iyyar wanda yayi Magana da manema labarai ya bayyana cewa shugaban jam’iyyar PDP ya yi bayani abubuwan da sukeyi kan shirye-shiyen zaben gwamnan jihar Osun da Ekiti.

Da dumi-dumi: Uche Secondus, IBB sunyi ganawar sirri

Da dumi-dumi: Uche Secondus, IBB sunyi ganawar sirri

Sauran mambobin da suka halarci taron sun kunshi kakakin jam’iyyar Kola Ologbodinyan, Alhaji Abdullahi Maibasira, da shugaban matan jam’iyyar.

Jam'iyyar PDP dai tana cigaba da kokarin farfadowa da kuma dinke barakar da ke cikinta gabanin zaben 2019 saboda su samu nasarar kwace shugabanci daga hannun jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Buhari ya gana da Firam ministan Birtaniya, Theresa May

Kwanakin baya, shugaban jam'iyyar ya baiwa yan Najeriya hakuri kan irin almundahana da babakeren da sukayi yayinda suke rike da ragamar mulki. Kana wasu daga cikinsu na tona asirin yadda suke magudin zabe a baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel