Likitoci da kwararru sun fadi yadda aka kashe mawakiyar nan da diyarta a Legas

Likitoci da kwararru sun fadi yadda aka kashe mawakiyar nan da diyarta a Legas

- Hukumar yan sanda ta jahar legos ta bayyana dalilin mutuwar mawaqiyar nan Zainab Nielsen ta rasa ranta ne a dalilin rauni da taji a sanadiyyar buguwa da kanta yayi

A ranar 5 ga watan afrilu ne aka sami gawar Zainab da yarta Petral 'yar shekaru hudu a Banana island Ekoyi inda take zaune tare da mijinta Peter Neilsen

Likitoci da kwararru sun fadi yadda aka kashe mawakiyar nan da diyarta a Legas

Likitoci da kwararru sun fadi yadda aka kashe mawakiyar nan da diyarta a Legas

Hukumar yan sanda ta jahar legos ta bayyana dalilin mutuwar mawaqiyar nan Zainab Nielsen ta rasa ranta ne a dalilin rauni da taji a sanadiyyar buguwa da kanta yayi.

A ranar 5 ga watan afrilu ne aka sami gawar Zainab da yarta Petral 'yar shekaru hudu a Banana island Ekoyi inda take zaune tare da mijinta Peter Neilsen.

Kwamishinan yan sandar jahar Edgal Imohimi ta bayyana cewa an sami alamun jini daga dakin marigayiyar zuwa kitchen duk da cewa anyi kokari wajen goge jinin. Har izuwa yanzu kwararru a wannan bangaren sunaci gaba da binciken.

Ya Kara da cewa an sami wani alamun jinin a gurin wanke hannu da kuma tawul wanda akayi amfani dashi bayan aikata kisan duk da shima anyi kokari wajen wankewa amma hakan bai hana kwararru ganowa ba.

DUBA WANNAN: Yadda kannen Amarya ke dana ango don gwada kwarinsa a wata kabila

Imohimi yace za'a tattara wadannan bayanai domin su zamo hujja akan wanda ake zargi wanda aka riga aka mika kotu.

Mr. Nielsen wanda aka Kama da laifin kashe matarsa da yarsa yayi kokarin maida kisan a matsayin hatsari.

Kwamishinan ya bada umarnin Kama wasu mutum biyar da ake zargin da sa hannun su a cikin lamarin a Ikorodu jihar legas.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel