2019: Ba tazarcen ta dame ni ba, manyan abubuwan nan biyu su suka addabe ni - Shugaba Buhari ga Theresa May ta Ingila

2019: Ba tazarcen ta dame ni ba, manyan abubuwan nan biyu su suka addabe ni - Shugaba Buhari ga Theresa May ta Ingila

- Tunawa da cewa Najeriya da Birtaniya na da hadin kai a abubuwa da dama tun a baya

- Al'amuran tsaro da tattalin arziki su suka dame ni ba zaben 2019 ba-inji Buhari

- Tsaro da Tattalin arziki su na sanya gaba

2019: Ba tazarcen ta dame ni ba, manyan abubuwan nan biyu su suka addabe ni - Shugaba Buhari

2019: Ba tazarcen ta dame ni ba, manyan abubuwan nan biyu su suka addabe ni - Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

Abubuwa guda uku da gwamnati mai ci a yanzu ta sa a gaba sune suka fi damuna inji shugaba muhammadu Buhari a yayin da suka yi taro da shugabar kasar birtaniya, Theresa May a ranar litinin a Downing Street da ke birnin Landan.

"Munyi kamfen ne akan abubuwa muhimmai guda uku. Tsaron kasar, farfado da tattalin arziki da kuma yaki da rashawa" inji shugaban kasa.

"Muna da zabe shekara mai zuwa, tunanin yan'siyasa duk ya koma kan zaben amma ni abinda yafi damuna shi ne tsaro da tattalin arziki"

Shugaba Buhari yace "Ina kara jinjiinawa Birtaniya saboda ta rike kawancen mu da kuma kamfanoninsu kamar Unilever, Cadbury da sauran su. Amma Oliver Twist, muna rokon karin hannayen jari. Muna godiya bisa ga horar da sojojin mu da sukeyi don fada da ta'addanci. Amma muna so mu cigaba da cinikayya daku da kuma karin hannayen jari."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da shugaba May akan cigaban da aka samu akan noma da kiwo wanda yace Najeriya zata tsaya da kafafunta a harkar abinci.

"Ina farincikin nasarar da muka samu a noma da kiwo. Mun rage shigo da shinkafa kashi 90 a cikin dari, mun adana da yawa don cinikayya tsakanin kasa da kasa kuma mun samar da aikin yi. Mutane da yawa suna gudu birni don samun kudin mai a maimakon noma.Amma yanzu duk sun koma gona. Gaskiya muna samun cigaba ta bangaren Tsaron abinci"

A harkar ilimi kuwa, shugaban kasa Muhammadu Buhari yace ana kara hannayen jari a kai, saboda mutane zasu iya kulawa da kansu Idan suna da ilimi a wannan zamanin na kimiyya da fasaha. Ilimi yana da matukar amfani."

Shugaba May, a jawabin ta tace, Birtaniya zata cigaba da aiki da Najeriya ta fannin horar da sojojinsu da kuma samar da makamai.

DUBA WANNAN: Yadda kannen Amarya ke dana ango don gwada kwarinsa a wata kabila

Akan sace yan' matan makarantar Chibok da yan'ta'addan Boko Haram sukayi kuwa, tace Birtaniya zata cigaba da baya Najeriya duk goyon bayan da take bukata. Tace gwamnatin Buhari tana samun cigaba akan tattalin arziki kuma ta shawarce shi da ya maida hankali duk da kusantowar zabe.

A bangaren ilimi kuwa tace yana da muhimmanci a ilimantar da yara saboda gobe. Sannan kuma babban makami ne na yaki da talauci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel