Abubuwan da aka tattauna kan APC 2019 tsakanin Buhari da Tinubu

Abubuwan da aka tattauna kan APC 2019 tsakanin Buhari da Tinubu

- A baya dai an sa rai Tinubu ne zai marawa shugaba Buhari a tikiti 2015

- Musulmi-Musulmi basu tsaya wa takara a baya, amma kamar hakan zata canja

- Babu alamar za'a tafi da Tunde Bakare ko Yemi Osinbajo

Abubuwan da aka tattauna kan APC 2019 tsakanin Buhari da Tinubu

Abubuwan da aka tattauna kan APC 2019 tsakanin Buhari da Tinubu

A ranar Lahadin ne dai kuma APC ta fitar da jerin sunayen wadanda za su shirya babban taron jam'iyyar, karkashin jagorancin Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa.

Sai kuma aka jiyo hadimin shugaba Buhari Bashir Ahmad, na bayanin an tattauna tsakanin shugaba Buhari da jagoran Yammacin Najeriya a siyasa, Bola Tinubu.

A baya dai shugaba Buhari ya mikawa Tinubun wuka da nama kan batun wanda zai zama mataimakinsa a 2015, inda ake sa rai Tinubun zai nuna ksa, amma saboda a lokacin akwai babban yaki a gaba, na korar PDP, sai yaki.

Yaqi ne saboda siyasar Najeriya bata barin manyan shugabannin kasar su zamo daga addini ko kabila daya, ko ma bangare daya, dole aka yi 'aure' da Buhari da Pastor Onbajo, aka rufe wa PDP baki, mai batun cewa APC jam'iyya ce ta masu shariar Islama.

DUBA WANNAN: Yadda kannen Amarya ke dana ango don gwada kwarinsa a wata kabila

Tabbas dai yanzu zayyi wuya shugaba Buhari ya tafi da Osinbajo, in ma kuma ya tafi dashi, har aka samu aka zarce, ana sa rai shgaban zai ajje shi ya dauki Tinubun domin shima yasanya rigar mataimakin shugaban kasa, kamar yadda aka sa rai tun zamanin CPC a 2010-2011.

A watan Fabrairu ne shugaban Buhari ya sanya Tinubu, a matsayin mutumin da zai jagoranci yunkurin da ake yi na dinke barakar da ke jam'iyyar APC.

Wasu masana harkokin siyasa suna kallon batun a wani gagarumin aiki da ba a taba yi ba a kasar ta fuskar rikicin siyasar cikin gida.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel