Yanzu-yanzu: Jam'iiyar APC ta saki jadawalin zabubbuka da taron gangaminta

Yanzu-yanzu: Jam'iiyar APC ta saki jadawalin zabubbuka da taron gangaminta

Jam'iyyar All Progressives COngress, APC, ta saki jadawalin zabubbukan shugabannin jam'iyyar da kuma na taron gangaminta inda za'a zabi sabbin shugabannin jam'iyyar na kasa ga baki daya.

A jiya Lahadi, jam'iyyar ta saki jerin mambobin kwamitin shirya taron gangamin wanda gwamnan jihar Jigawa, Mohammad Baaru, ke jagoranta tare gwamnan jihar Ono, Rotimi Akeredolu, a matsayin mataimakinsa.

Ga yadda za'a gudanar da su:

1. Zaben shugabannin unguwanni , 5 ga watan Mayu 2018

2. Zaben shugababub kananan hukumomi: 12 ga watan Mayi, 2018

3. Zaben shugabannin jam'iyyar a jihohi: 19 ga watan Mayu, 2018

4. Taron gangami da zaben shugabbanin jam'iyyar na kasa: 23 ga watan Yuni, 2018.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel