Akwai sa hannun Gwamnoni wajen rikicin Makiyaya Inji Kungiyar da kare-hakkin Jama’a

Akwai sa hannun Gwamnoni wajen rikicin Makiyaya Inji Kungiyar da kare-hakkin Jama’a

Wata kungiya da ke karkashin Hukumar da ke kula da hakkin ‘Yan Adam a Najeriya tayi nazarin rikicin da ake samu tsakanin Makiyaya da Manoma kwanaki inda aka gano cewa akwai Shugabannin da su ka hura wutan rikicin kuma su ka labe su na kuka.

Wani bincike da Kungiyar da ke lura da hakkin Bil Adama a kasar ta gudanar da ake sa rai babu son kai ya bayyana cewa Gwamnonin Jihar Taraba da Jihar Benuwe sun yi sake wajen maganin rikicin Makiya wanda har abin ya kai inda ya kai a halin yanzu.

Akwai sa hannun Gwamnoni wajen rikicin Makiyaya Inji Kungiyar da kare-hakkin Jama’a

Jama'a wajen wani taro game da rikicin Makiyaya a Najeriya. Hoto daga: Daily Nigerian

Kamar yadda mu ka samu wani dogon rahoto daga Jaridar Daily Nigeria, Kungiyar da ke kare hakkin jama’a tace Gwamnonin wadannan Jihohi ba su dauki matakan da su ka dace na tsare rayukan jama’a ba wanda hakan ya Sojoji su ka dauki matakin da ya dace.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi ba - ta -kashi da jama'a a Banuwe

Sai dai kuma wadannan Gwamnonin ne su ka koma gefe su na kukan cewa babu adalci a lamarin Sojojin kasar. Shugaban Kungiyar da ta gudanar da wannan bincike Barista Maxwell Gowon yace akwai rashin adalci da zalunci a game da batun daga Gwamnonin.

Gowon ya bayyana cewa sun yi hira da wadanda rikicin Makiyayan ya shafa a irin su Jihar Taraba, Filato, Adamawa, Kogi, Nasarawa da ma Benuwe inda aka gano cewa Rundunar Soji sun taimaka wajen kashe wutar fitinar yayin da Shugabannin Yankin su kayi ko oho .

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel