An kama wani likitan bogi da ko firamare bai kammala ba

An kama wani likitan bogi da ko firamare bai kammala ba

'Yan sanda a jihar Legas sun kama wani mutum, Abdulrahman Mohammed, bisa zargin sa da sojan gona a matsayin likita na tsawon shekaru hudu.

A cewar hukumar 'yan sanda a jihar, Abdulrahman, ya mallaki wani asibiti mai zaman kansa inda ya shafe fiye da shekaru hudu yana duba jama'a a unguwar Idi-Araba dake yankin Mushin a garin Legas.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Legas, Imohimi Edgal, ya ce Abdulrahman har allura yake yiwa jama'a a jijiya tare da karbar samfurin fitsari da na jini domin gudanar da bincike ga marasa lafiya.

An kama wani likitan bogi da ko firamare bai kammala ba

An kama wani likitan bogi da ko firamare bai kammala ba

Kwamishinan ya kara da cewar, tuni wanda suke tuhuma, Abdulrahman, ya amsa laifin sa tare da sanar da hukuma cewar yana sayo magungunan da yake amfani da su ne a Idumota.

DUBA WANNAN: 'Yan fashi sun gamu da fushin 'yan sanda bayan sace motar haya makare da fasinjoji a Legas

Da yake magana da manema labarai, Abdulrahman, ya ce, "Na kasance mai tallar magani kafin daga bisani na bude shagon sayar da magunguna.

Ko makarantar firamare ban kammala ba balle na samu izinin bude shagon magani ko duba marasa lafiya.

Ya kara da cewar, ba shine ke karbar samfurin fitsari da na jinin ba, illa iyaka dai yana sayar da kayan yin gwaje-gwajen ne tare da bayyana cewar ya kan gwada marasa kafin ya basu magani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel