Siyasar Kano: Bayan wata 11 da tsige shi matsayin lamba1 yau an nada shi a matsayin lamba 2

Siyasar Kano: Bayan wata 11 da tsige shi matsayin lamba1 yau an nada shi a matsayin lamba 2

- Da alama rikicin da ya kunno kai a Majalisar Dokoki ta jihar Kano zai lafa bayan da shugaban Majalisar ya tsallake rijiya da baya

- Sauran kiris a tsige kakakin Majalisar a jiya, amma yau ta bayyana cewa ya sha da kyar

- Kuma wani abin mamaki ya faru da daya daga cikin sabbin wadanda aka nada bayan sauke tsoffin mambobin daga mukaminsu

A yau Alhamis Majalisar Dokokin jaihar Kano ta dawo da zamanta bayan wata goguwar sauyi da ta kada wadda tayi sandiyyar sauke wasu manyan ‘yan Majalisar daga mukamansu ta kuma kusa tafiya da shugaban Majilisar Yusuf Abdullahi Atah.

Siyasar Kano sai Kano: Bayan wata 11 da tsige shi a matsayin lamba 1 yau an nada shi a matsayin lamba 2

Yusuf Abdullahi Atah

Shugaban Majalisar Yusuf Abdullahi Atah ne ya rantsar da sabbin wadanda aka nada ciki har da tsohon shugaban Majalisar da aka tsige kusan kimanin shekara guda da ta wuce Kabiru Alhasan Rurum a matsayin sabon mataimakin shugaban Majalisar.

Zaman Majlisar da ya gudana da misalin 11: 30am na safe da mambobin Majalisar 36 suka halarta ‘yan bangaren tsagin kwankwasiyya da Gandujiyya da kuma wani dan jam’iyyar PDP daya tilo Abdullahi Muhammad Chiromawa.

KU KARANTA: Da dumin-dumi: Harin kunar bakin wake a masallaci ya hallaka mutane hudu a Maiduguri

Majiyarmu ta rawaito cewa zaman Majalisar dai bai wuce na kimanin awa guda ba, kuma an ga ‘yan Majalisar suna ta raha da juna kamar ba abinda ya faru tsakanisu.

Daga cikin wadanda aka rantsar yau sun hada da Muhammad Bello Butu butu a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye da kuma Baffa Danagundi a matsayin Bulaliyar Majalisar da Sanusi bataitya da kuma Ayuba Labaran Durum.

Ana shi jawabin bayan kamala rantsuwa sabon mataimakin shugaban Majalisar Alhasan Rurum cewa yayi, zai yi iya kokarinsa wajen sauke nauyin da aka daura masa kamar yadda ya saba, kana ya godewa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje bisa shiga tsakani da yayi domin sasanta lamarin.

Siyasar Kano sai Kano: Bayan wata 11 da tsige shi a matsayin lamba 1 yau an nada shi a matsayin lamba 2

Alhasan Rurum

“Yau Alhamis na cika watanni 11 da sauka daga mukamin kakakin Majalisar, sai kuma ga shi yau an rantsar da ni a matsayin mataimakin shugaba.” A cewar sabon mataimakin kakakin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel