Babban lauya Falana ya jinjinawa mabiya Shi'a, ya basu wata shawara

Babban lauya Falana ya jinjinawa mabiya Shi'a, ya basu wata shawara

Babban lauya mai daraja ta daya (SAN) kuma mai rajin kare hakkin bil'adama, Femi Falana, jinjinawa mabiya Shi'a bisa kafewar su a kan sai an saki shugaban su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Gwamnatin tarayya ta tsare El-Zakzaky da mai dakinsa tun shekarar 2015 biyo bayan wata hatsaniya tsakanin magoya bayansa da dakarun sojin Najeriya.

Tun bayan kamun da aka yi masa magoya bayansa ke gudanar da zanga-zanga a garuruwa daban-daban domin neman a sako shi.

Babban lauya Falana ya jinjinawa mabiya Shi'a, ya basu wata shawara

Babban lauya Falana da Sheikh El-Zakzaky

Da yake aike sakon nuna goyon baya ga mabiya Shi'a, Falana, ya bayyana cewar zanga-zangar magoya bayan El-Zakzaky bata saba da kundin tsarin mulkin Najeriya ba da ya bawa 'yan kasa damar bayyana ra'ayin su da yin gangami cikin salama ba.

Falana ya kara da cewa, "abinda ku ke yi dai-dai ne, yaki ne da danniya da kuma cin zali da gwamnatin tarayya tayi maku."

DUBA WANNAN: Sheikh El-Zakzaky: Magoya bayan Shi'a sun mamaye manyan titunan Abuja

Kazalika ya bukaci mabiya Shi'ar da kada su razana balle har ta kai ga sun hakura da zanga-zangar neman hakkin su tare da shaida masu cewar ta hanyar zanga-zangar ne kawai zasu samu biyan bukatar su tunda gwamnatin tarayya ta ki yin biyayya ga umarnin kotu da ya ce ta saki Sheikh El-Zakzaky.

A yau ne dai ta rincabe tsakanin jami'an 'yan sandan Najeriya da mabiya Shi'a bayan da zanga-zangar da suke gudanarwa a birnin tarayya, Abuja, ke neman tsayar da al'amura a kwaryar birnin garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel