'Yan fashi sun gamu da fushin 'yan sanda bayan sace motar haya makare da fasinjoji a Legas

'Yan fashi sun gamu da fushin 'yan sanda bayan sace motar haya makare da fasinjoji a Legas

Jami'an 'yan sandan ko-ta-kwana a jihar Legas sun saka wasu 'yan fashi da makami guduwa su bar motar haya dauke da fasinjoji da suka sace.

'Yan fashin guda hudu sun shiga motar hayar dake tafiya jami'ar LASU daga Iyana Ipaja amma sai suka kwace motar yayin da motar ta tsaya domin wani fasinja zai sauka a rukunin gidajen Diamond dake unguwar Isheri.

Direban motar, Sheriff Dada, ya ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis da misalin karfe 11:00 na dare.

'Yan fashi sun gamu da fushin 'yan sanda bayan sace motar haya makare da fasinjoji a Legas

Motar hayar da 'yan fashin suka kwace

Direban motar ya ce, "bayan 'yan fashin sun dora min bindiga a ka, sai suka fara binciken jakankunan fasinjoji suna dauke wayoyin hannu da kudi. Ana hakan ne sai kwandasta na ya samu ya sulale kafin nima su wurgo ni daga motar bayan sun hangi motar 'yan sanda a gaban mu."

DUBA WANNAN: An samu gawar jaririn wata takwas a cikin robar ajiye ruwa bayan an rasa shi na kwana guda

Kwandastan motar, Hakeem Hassan, ya ce, duk da 'yan fashin sun yi barazanar harbin sa hakan bai hana shi guduwa ba.

Bayan nasarar cafke 'yan fashin, jami'an 'yan sanda sun sami wata karamar bindiga ta gida da kuma wata wayar hannu. Kazalika sun mayar wa duk wanda aka yiwa kwace kayan sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel