Baki shi ke yanka wuya: Wani matashi ya sha bulalar kazafi 80 sakamakon aibanta sirikarsa da sunan ‘Karuwa’

Baki shi ke yanka wuya: Wani matashi ya sha bulalar kazafi 80 sakamakon aibanta sirikarsa da sunan ‘Karuwa’

Wata Kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a unguwar Magajin Gari ta jihar Kaduna ta yanke ma wani matashi mai suna Shuaibu Umar hukuncin bulala tamanin, 80, sakamakon kirar matar yayansa, Suwaiba Abdulkadir da yayi suna Karuwa.

Suwaiba ta kai karar Shuaibu ne kan tuhumarsa da take yi da cin zarafinta tare da yi mata kazafi, bayan da ya kirata a suna Karuwa, sakamakon wata yar sa’in’sa da suka samu, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

KU KARANTA: Filla filla: Yadda Sanatoci ke bindiga da kudaden garabasa da suke samu a majalisar dattawa

“Shuaibu kanin mijina ne, kum da fari mun samu matsala da juna ne, wanda ta kai ga mun yi cacar baki, ana ciin haka kwatsam sai na ji ya kira ni da suna ‘Karuwa’, inda ya zarge ni da karuwanci, don haka nake bukatar wannan Kotu mai adalci ta duba kuka na, a bi min hakkina, don kuwa ya bata min suna.” Inji Suwaiba.

Baki shi ke yanka wuya: Wani matashi ya sha bulalar kazafi 80 sakamakon aibanta sirikarsa da sunan ‘Karuwa’

Bulala

Sai dai Shuaibu bai musanta tuhumar da surukarsa ke yi masa ba, inda yace ya furta hakan ne cikin bacin rai, kuma bai yi nadamar furta Kalmar ba; “Ita ta fara kirana da Barawo dan shaye shaye, hakan yayi matukar bata min rai, ni kuma na ce mata Karuwa, kuma bana nadamar abin da na fada.”

Majiyar Legit.ng ta ruwaito bayan jin bayanan kowanni bangare, sai Alkalin Kotun Mallam Dahiru Lawal ya umarci a bullae matashin bulala tamanin sakamakon kin hanye kalaman da ya furta game da surukar tasa.

“Wannan hukunci da ni Dahiru Lawal na yanke yayi daidai da koyarwar Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbatar a gare shi, inda ya hana yi ma wani ko wata kazafin zina, har sai ya kawo shaidu guda hudu da su kama mutumin dayake zargi turmi da tabarya.” Inji Alkali.

Ba tare da bata lokaci ba kuwa aka kwantar da Shuaibu a bainar jama’a, inda aka dinga shauda masa dorina har sau tamanin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel