Yan bindiga sun yi ba-ta-kashi da Yansanda a Benuwe, sun hallaka Yansanda 4

Yan bindiga sun yi ba-ta-kashi da Yansanda a Benuwe, sun hallaka Yansanda 4

Rundunar Yansandan jihar Benuwe ta tabbatar da mutuwar jami’an Yansandan guda hudu a hannun yan wasu yan bindiga da suka kai musu farmaki, da ake zargin makiyaya ne, inji rahoton Punch.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Moses Yamu ne ya sanar da haka a ranar Litinin 16 ga watan Afrilu, inda yace lamarin ya faru ne a kauyen Anyibe dake cikin karamar hukumar Logo na jihar.

KU KARANTA: Buhari ya kammala aikin jirgin kasa na babban birnin tarayya Abuja, zai fara aiki (Hotuna)

Jaridar Punch ta ruwaito garuruwan Logo da Guma na fuskantar matsanancin matsalar tsaro sakamakon hare haren makiyaya yan bindiga tun a farkon shekarar nan, wand hakan yayi sanadin salwantar rayuka da dama.

Yan bindiga sun yi ba-ta-kashi da Yansanda a Benuwe, sun hallaka Yansanda 4

Babban Sufetan Yansanda

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakaki Yamu na cewa yan bindigar sun yi ma Yansandan kwantan bauna ne da misalin karfe shidda na yammacin Lahadi 15 ga watan Afrilu, har zuwa safiyar Litinin, 16 ga watan Afrilu.

“Abin takaici da ban tausayi shi ne sun kashe mana jami’ai guda hudu.” Inji shi, sai dai yace rundunar ta aika da karin jami’an Yansanda ta sama ta kasa don tabbatar da tsaro a yankin, a sakamakon zaman dar dar a tsakanin jama’an kauyen da daya biyo bayan harin.

Daga karshe Kaakakin ya bada tabbacin Yansanda zasu kamo yan bindigar, inda yace a yanzu haka jami’an hukumomin tsaro daban daban sun bazama suna farautar yan bindiga ruwa a jallo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel