Yan majalisar wakilai sun watsar da ayyukansu a kokarin neman komawa kan kujerunsu

Yan majalisar wakilai sun watsar da ayyukansu a kokarin neman komawa kan kujerunsu

- ‘Yan Majalisar Wakilai sun shiga yakin neman zabe don komawa kan kujerunsu a shekarar 2019, sun watsar da ayyukansu na majalissar

- Zaben wanda yanzu sauran watanni 10, amma dayawa cikin ‘yan majalisar basu da tabbacin komawa kan kujerun nasu tun a zaben jam’iyya na primaries ba, wanda ke zuwa

- Bincike ya nuna cewa yawancin ‘yan majalisar sun watsar da ayyukansu na majalisar sun mayar da hankalinsu a kan neman a sake tsayar dasu takara a jam’iyyun nasu

‘Yan Majalisar Wakilai sun shiga yakin neman zabe don komawa kan kujerunsu a shekarar 2019, sun watsar da ayyukansu na majalissar.

Zaben wanda yanzu sauran watanni 10, amma dayawa cikin ‘yan majalisar basu da tabbacin komawa kan kujerun nasu tun a zaben jam’iyya na primaries ba, wanda ke zuwa na 2019.

Bincike ya nuna cewa yawancin ‘yan majalisar sun watsar da ayyukansu na majalisar sun mayar da hankalinsu a kan neman a sake tsayar dasu takara a jam’iyyun nasu, don komawa matsayin da suke a kai yanzu.

Yan majalisar wakilai sun watsar da ayyukansu a kokarin neman komawa kan kujerunsu

Yan majalisar wakilai sun watsar da ayyukansu a kokarin neman komawa kan kujerunsu

Daya daga cikin manyan jami’an majalisar ya bayyanawa manema labarai na The PUNCH, a birnin tarayya cewa shugaban majalissar Yakubu Dogara wanda ya fara yiwa kansa kamfen don sake komawa tasa kujerar ta shugaban majalisar, ya fahimci ragowa sosai a halartar taron majalisar daga ‘yan majalissar.

KU KARANTA KUMA: Barayi kadai ke zama shuwagabannin kasa a Najeriya- Balarabe Musa

Bincike ya nuna cewa kusan 223 cikin ‘yan majalisar ta 7 daga 2011 zuwa 2015 basu koma kan kujerun nasu ba a zaben ‘yan majalisar da akayi na 8, wanda yawanci wasu tun zaben jam’iyya suka fadi wasu kuma sun fadi a babban zabe na shekarar ta 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel