Wani matashi ya kashe budurwarsa saboda ta samu ciki

Wani matashi ya kashe budurwarsa saboda ta samu ciki

- Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Filato ta kama wani matukin babur Stephen Gyang, bisa ga zargin kisan budurwarsa Alice Samuel

- Gyang ya kashe budurwar tasa sakamakon ta jingina cikin da take dauke dashi a gareshi

- Gyang mai shekaru 20 yace ya kashe budurwar tasa saboda tun farko tace cikin ba nasa bane, sai daga baya mahaifiyarta ta turo ta saboda tanaso na dauki nauyin yarinyar shiyasa tace ta lakaba mani cikin

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Filato ta kama wani matukin babur Stephen Gyang, bisa ga zargin kisan budurwarsa Alice Samuel. Ya kashe budurwar tasa sakamakon ta jingina cikin da take dauke dashi a gareshi.

Gyang mai shekaru 20 yace ya kashe budurwar tasa saboda tun farko tace cikin ba nasa bane, sai daga baya mahaifiyarta ta turo ta saboda tanaso na dauki nauyin yarinyar shiyasa tace ta lakaba mani cikin.

Wani matashi ya kashe budurwarsa saboda ta samu ciki

Wani matashi ya kashe budurwarsa saboda ta samu ciki

Kwamishinan ‘Yan Sanda, Undie Adie, yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ana shirin gurfanar dashi a gaban kotu. Lamarin ya faru ne a kauyen Tahoss, dake karamar hukumar Riyom a jihar Filato.

KU KARANTA KUMA: Dalilin gayyatar da Trump yayiwa Buhari zuwa Washington

Abokin ta’addancin nasa Kelly James dan shekara 20 wanda shine shaida, ya bayyana cewa ya roki Gyang da kada ya kasheta amma ya kiya, a karshe ma yace wanda ake zargin ya masa barazana a kan zai kasheshi shima idan bai tayashi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel