Fallasa: An tafka magudi a zaben 2015 a arewa - Dattijo Tanko Yakasai

Fallasa: An tafka magudi a zaben 2015 a arewa - Dattijo Tanko Yakasai

Dattijo kuma babban dan siyasa a kasar nan, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana zaben baidaya na shekarar 2015 da cewa an tafka gagarumin magudi a arewacin Nigeria.

Yakasai, ya bayyana haka ne ga y'an jarida, yayin da ya jagoranci tawagar wasu daga shugabannin arewa da y'an majilasar dokokin arewa zuwa gidan tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida a gidan sa dake Minnan babban birnin jahar Niger, jiya Lahadi.

Cikin bayaninsa, Tanko Yakasai yace: "Lokacin da aka gabatar da sabuwar hikimar yin zabe shekarar 2015, na yi maraba da ita sosai, bayan zaben na fahimci irin ta'asar da aka tafka.

Fallasa: An tafka magudi a zaben 2015 a arewa - Dattijo Tanko Yakasai

Dattijo Tanko Yakasai

"An bi hanyoyin magudi da yawa. Abinda ya faru a 2015, inda yan kudu suka rinka tserewa yankinsu tsoron abinda ka-je-ya-zo, suka bar gun da suka yi rijistar zabe, suka tafi inda ba can suka yi rijista ba, ba kuma za su iya yin zabe a can ba, wannan ma hanyar tafka magudi ce.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya bayyana mutanen da suka jefa 'yan Najeriya cikin fatara talauci

Wata hanyar kuma dai ita ce, yan kudun da ba su gudu ba, sun gaza iya fitowa rumfunan zabe lokacin da ake kada kuri'a. Saboda furgicin za'a iya far musu. Don haka suka hakura da zaban wanda suke so ya zama shugaban kasa. Wannan ma hanyar magudi ce.

Yakasai ya ce, makasudin ziyarar su zuwa gidan tsohon shugaban kasa, don sanar da shi burin tawagar ta su na ganin hadin kai da cigaban yankin Arewa. A nasa bangaren, tsohon shugaban kasar, ya yaba da irin namijin kokarin su, ya kuma basu tabbacin goyon bayansa don ganin hadin kan kasa baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel