Dalilin gayyatar da Trump yayiwa Buhari zuwa Washington

Dalilin gayyatar da Trump yayiwa Buhari zuwa Washington

- Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zaya gana da Donald Trump a Washington don tattaunawa gaem da yanda za’a magance ta’addanci da kuma kawo cigaban tattalin arziki

- Bayanin yazo ne bayan cika shekaru hudu da kungiyar Boko Haram suka sace ‘yan matan makarantar Chibok

- Ziyarar Shugaba Buhari a White House dake Washington ya kasance sakamakon alkawarin da Rex Tillerson tsohon Sakataren kasar ta Amruka yayiwa Najeriya game da ceto ‘yan matan Chibok

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zaya gana da Donald Trump a Washington don tattaunawa game da yadda za’a magance ta’addanci da kuma kawo cigaban tattalin arziki, cikin abubuwan da zasu tattauna.

Bayanin yazo ne bayan cika shekaru hudu da kungiyar Boko Haram suka sace ‘yan matan makarantar Chibok. Duk da kasancewar Najeriya kasar data fi kowace tattalin arziki Afirika ta Yamma, tana cikin kasashen dake fama da matsalar tsaro.

Dalilin gayyatar da Trump yayiwa Buhari zuwa Washington

Dalilin gayyatar da Trump yayiwa Buhari zuwa Washington

Ziyarar Shugaba Buhari a White House dake Washington ya kasance sakamakon alkawarin da Rex Tillerson tsohon Sakataren kasar ta Amruka yayiwa Najeriya game da ceto ‘yan matan Chibok.

KU KARANTA KUMA: Mahaifina ya kona mani kaya saboda na yarda da Yesu Almasihu - Sanata Binta

Tillerson kafin korar da kasar ta Amuruka tayi masa a watan Janairu, yace zasu bawa Najeriya tallafin makaman da ake bukata don a yaki ‘yan ta’addan a ceto ‘yan matan makarantar ta Chibok wadan da suka rage a hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel