2019: Bamu yanke hukunci akan Buhari ba game da zaben shugaban kasa – Kungiyar yan Arewa

2019: Bamu yanke hukunci akan Buhari ba game da zaben shugaban kasa – Kungiyar yan Arewa

- Kungiyar ‘yan Arewa ta ACF a jiya ta bayyana cewa a duk cikin kungiyoyin dake Arewa masu zaman kansu, sune kadai zasu iya bayyana sakamakon tsayawar Muhammadu Buhari takara a zaben 2019

- Kungiyar kuma tace duk wadanda ke maganganu game da ayyukan Buhari da kuma damar da yake da ita game da zaben mai zuwa sunayi don kansu ne kawai, bamu ciki

- Ibrahim Commassie, tsohon shugaban hukumar ‘Yan Sanda na kasa shine ciyaman na kungiyar, yace ‘yan Najeriya su saurara suji wanda kungiyar zata tsaida shine wanda ya kamata su zaba

Kungiyar ‘yan Arewa ta ACF a jiya ta bayyana cewa a duk cikin kungiyoyin dake Arewa masu zaman kansu, sune kadai zasu iya bayyana sakamakon tsayawar Muhammadu Buhari takara a zaben 2019.

Kungiyar kuma tace duk wadanda ke maganganu game da ayyukan Buhari da kuma damar da yake da ita game da zaben mai zuwa sunayi don kansu ne kawai, bamu ciki. Ya bayyana hakane lokacin da yake zantawa da New Telegraph a gidansa dake jihar Katsina.

Ibrahim Commassie, tsohon shugaban hukumar ‘Yan Sanda na kasa shine ciyaman na kungiyar, yace ‘yan Najeriya su saurara suji wanda kungiyar zata tsaida shine wanda ya kamata su zaba. Yace duk wadanda ke wadansu maganganu suna fadar ra’ayinsu kawai ban a kungiya ba.

2019: Bamu yanke hukunci akan Buhari ba game da zaben shugaban kasa – Kungiyar yan Arewa

2019: Bamu yanke hukunci akan Buhari ba game da zaben shugaban kasa – Kungiyar yan Arewa

Yace “shekarar 2015, nine na jagoranci lamarin”. Munce dole shuwagabanci ya dawo Arewa, kuma mukace duk jam’iyyar data tsayar da dan Arewa ita zamu zaba. Sai APC ta tsayar da Buhari “kuma na fito na fadawa mutane mu hadu mu goya masa baya kuma akayi hakan”.

KU KARANTA KUMA: 2019: Atiku ya kai ziyara kasar Ingila don ya karo suna

Tsohon shugaban hukumar ‘Yan Sandan yace kungiyar tana jira ne kowace jam’iyya ta fitar da nata dan takarar kafin kungiyar tasu ta bayyanawa jama’a wanda zasu zaba a zaben na 2019 mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel