2019: Atiku ya kai ziyara kasar Ingila don ya karo suna

2019: Atiku ya kai ziyara kasar Ingila don ya karo suna

- Tsohon mataimakin shugaban kasa ya fara kamfen don gyaran sunan da aka bata masa a shekarun baya

- Ya fara kamfen din ne a kasar Ingila don neman shawarta akan yanda zai gyara sunansa da aka bata sakamakon ya bayyana tsayawarsa takarar shugaban kasa a shekarar 2019

- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shine wanda ya bayyana cewa Atiku yana aikata rashawa, wanda shine dalilin da yasa suka raba hanya a shekarar 2003

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya fara kamfen don gyaran sunan da aka bata masa a shekarun baya, lokacinda ya sauka daga kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Ya fara kamfen din ne a kasar Ingila don neman shawarta akan yanda zai gyara sunansa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bata masa.

Yayi hakanne sakamakon ya bayyana kudurinsa na tsayawarsa takarar shugaban kasa a shekarar 2019, karkashin jam’iyyar PDP, wanda majiyar Thisday ta kusa dashi ta bayyana cewa ba zai wuce karshen watan Mayu ba zaya bayyanawa jam’iyyar.

2019: Atiku ya kai ziyara kasar Ingila don ya karo suna

2019: Atiku ya kai ziyara kasar Ingila don ya karo suna

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shine wanda ya bayyana cewa Atiku yana aikata rashawa, wanda shine dalilin da yasa suka raba hanya a shekarar 2003, lokacin da suka nemi tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyya daya, inda ya fadi zaben jam’iyyar na primary.

KU KARANTA KUMA: Ku jira shugabancin 2023 domin bazaku iya da Buhari ba – Tsohon gwamna a mulkin soja ga Atiku da sauran masu neman takara

Ziyarar wadda ya kai ta kwanaki uku, yayita ne don ganawa da ‘yan Najeriya mazauna kasar ta Ingila, a garin London, don kara nemo masu basira na kasar mu, don karfafa tattalin arzikin kasar mu.

Ana sauraren dawowarsa farkon wata mai kamawa don ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP don su bayyana manufarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar ta PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel