Takarar Shugaban kasa: Balarabe Musa ya nemi Sowore ya shigo Jam’iyyar PRP

Takarar Shugaban kasa: Balarabe Musa ya nemi Sowore ya shigo Jam’iyyar PRP

- Omoyele Sowore ya bayyana cewa zai yi takarar Shugaban kasa a 2019

- Jam’iyyar PRP tayi masa tayin kujerar Shugaban kasar a karkashin ta

- Balarabe Musa yace a shirya su ke su hada-karfi domin kada APC a 2019

Shugaban Jam’iyyar PRP Alhaji Balarabe Musa ya gana da Omoyele Sowore a gidan sa da ke Garin Kaduna a Ranar Juma’a inda ya nuna cewa a shirya su ke da su ba shi takarar kujerar Shugaban kasa a zaben 2019.

Takarar Shugaban kasa: Balarabe Musa ya nemi Sowore ya shigo Jam’iyyar PRP

Mai Sahara Reporters ya sha alwashin buge Buhari a 2019

Tsohon Gwamnan na Jihar Kaduna Balarabe Musa ya bayyana cewa su na neman ‘dan takara ne da zai fitar da Najeriya daga kuncin da jama’a su ka shiga. Alhaji Musa yace ana bukatar Matashi ne mai fada a-a ji a mulkin Najeriya.

KU KARANTA: Manyan kasar nan sun yi wani kus-kus a gidan IBB

Babban ‘Dan siyasan kasar yace Jam’iyyar PRP za ta hada kai da sauran Jam’iyyun kasar domin ganin an tika Shugaba Buhari da kasa kamar yadda Sowore ya ke buri. A jawabin na sa yayi fatali da yunkurin Obasanjo na 3rd force.

Balarabe Musa yayi wa Sowore wanda ke neman Shugaban kasa tayin Jam’iyyar su ta PRP wanda yace tana fafatuka ne wajen ganin zaman lafiya da dawo da martabar kasar da kuma adalcin rayuwa da habaka tattalin Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel