Fusatattun matasa sun kai farmaki wani masarauta, sun kora sarauniya

Fusatattun matasa sun kai farmaki wani masarauta, sun kora sarauniya

- Wasu fusatattun matasa sun kai farmaki masarautar Agbado-Ekiti, jihar Ekiti

- Matasan na adawa ne da sarauniyar da aka nada masu

A jiya 15 ga watan Afrilu wasu fusatattun matana a Agabado Ekiti, karamar hukumar Gbonyin dake jihar Ekiti, sun kai farmaki masarautar garin domin koran sarauniya, Bolaji Okunbobade, wanda a cewarsu dattawan garin suka daura ta karfin tuwo.

Vanguard ta ruwaito cewa dattawa ne suka zabi Okunbobade domin ta ci gaba da mulkin mahaifinta, marigayi, Owa Oro na Agbado, Oba Okunbobade.

Fusatattun matasa sun kai farmaki wani masarauta, sun kora sarauniya

Fusatattun matasa sun kai farmaki wani masarauta, sun kora sarauniya

Sai dai kuma matasan irate da suka mamaye hanyar Ado-Ikare da tsawon wasu sa’o’i sun zargi daga daga cikin dattawan, Cif Kayode Adeyeye, da zabar Bolaji a matsayin sarauniya ba tare da amincewar kowa ba.

KU KARANTA KUMA: Ku jira shugabancin 2023 domin bazaku iya da Buhari ba – Tsohon gwamna a mulkin soja ga Atiku da sauran masu neman takara

Sunyi zargin cewa ba’a bi hanyar da ya kamata ba sannan kuma dukkanin masu ruwa da tsaki basu da masaniya wajen zabar Bolaji wanda suka bayyana a matsayin sarauniya da bata cancanta ba.

Garin ya shiga hargitsi inda suka kora sarauniyar tare da hadimanta daga fadar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel