Matasa masu jini a jika sun fi himma wajen aiki – Inji El-Rufai

Matasa masu jini a jika sun fi himma wajen aiki – Inji El-Rufai

- Gwamna Nasir El-Rufai yace ya fi son aiki da matasa saboda kokarin su

- Gwamnatin Jihar Kaduna ta na yi sosai da matasa da kuma ‘yan mata

- Kwanan nan aka ba wasu mata manyan mukamai a Hukumomin Jihar

Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai ya bayyana babban dalilin da ya sa ya fi sha’awar aiki da Matasa masu matsakaicin shekaru a harkokin Gwamnati. Gwamnan dai yana damawa da Matasa sosai.

Gwamna El-Rufai yace masu kananan shekaru sun fi kwazo

Labari ya zo mana ta bakin Dr. Joe Abah wani tsohon babban Jami’in Gwamnati a Najeriya wanda ya bayyana abin da ya sa Gwamnan Kaduna ya fi ba Matasa mukamai a Gwamnati a shafin sa na sada zumunta na Tuwita.

KU KARANTA: Ta kashe Mahaifin ta saboda yana adawa da Saurayin ta

Gwamnan yace da gan-gan yake ware mukamai da dama ga Matasa musamman kuma mata domin sun fi kokari wajen aiki saboda karancin shekarun su. Yanzu haka dai Kwamishonin da ke Jihar Kaduna har 3 duk mata ne.

Kwanaki idan ba ku manta ba Gwamna El-Rufai ya nada Shugabannin Hukumar KADIPA da na KADSTRA wanda duk mata ya ba ofisoshin. Umma Aboki le rike da Hukumar KADIPA yayin da Aisha Saidu-Bala ke KADSTRA.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel