Yan bindiga sun bindige wani Dansanda a jihar Benuwe, Yansanda 11 sun yi ɓatar dabo

Yan bindiga sun bindige wani Dansanda a jihar Benuwe, Yansanda 11 sun yi ɓatar dabo

Akalla dansanda guda daya ne ya rasa ransa a sakamakon wani hari da yan bindiga suka kai a jihar Benuwe, wanda a yanzu haka yayi sanadiyyar bacewar mutane 11 da har yanzu ba’a san inda suke ba.

Premium Times ta ruwaito yan bindigar sun kashe dansandan da misalin karfe 6 na yamma a yayin da yake tafiya akan babur tare da wani abokin aikinsa daga Ayibe zuwa Ayilamo, a cikin karamar hukumar Logo.

KU KARANTA: An ja kunnen gwamnati game da shigo da amfanin gona da aka sarrafa su da ilimin kimiyya

“Sun hallaka Dansanda guda daya, yayin da gudan Dansandan ya tsira da harbin bindiga a jikinsa.” Kamar yadda wani mazaunin garin ya tabbatar ma majiyar Legit.ng a daren Litinin.

Yan bindiga sun bindige wani Dansanda a jihar Benuwe, Yansanda 11 sun yi ɓatar dabo

Yansanda

Sai dai bayan wannan hari da aka kai ma Yansandan, wasu Yansanda guda goma sha daya sun yi ta maza, inda suka bi sawun yan bindigar, ashe yan bindigar sun yi kwantar bauna, a yanzu haka babu tabbacin inda sauran 11 suke.

“Yanzu haka bamu san inda Yansanda 11 suke ba, ya kamata a tabbatar da yan bindigan nan a matsayin yan ta’adda, sun kona motar Yansanda guda 1.” Inji wani mazaunin garin.

Duk da cewa kwamishinan Yansandan jihar, Fatai Owoseni bai tabbatar da harin ba, wani babban Dansanda a Katsina Ala ya tabbatar da harin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel