Zaben 2019: Kawai ka manta da batun a sake zabenka

Zaben 2019: Kawai ka manta da batun a sake zabenka

- Da Buhari zai dauki shawara da ya sauya aniyarsa ta sake tsayawa takara 2019

- Muna bukatar shugaban da zai na daukar shawara mutane

Alhaji Ghali Umar Na’abba, tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa yace, shi bai ga wani abin kirkikin da Muhammadu Buhari yayi ba da har yake neman a sake zabensa a karo na biyu.

Zaben 2019: Kawai ka manta da batun a sake zabenka

Alhaji Ghali Umar Na'abba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai ya bayyana aniyasar ta sake tsayawa takara domin sake darewa shugabancin Najeriya a karo na biyu a 2019, a wani taro da kwamitin koli na jam’iyyar APC yayi.

A cewar shugaban ya zabi ya sake tsayawa takara ne a karo na biyu sakamakon yawaitar bukatar hakan da talakawa keyi domin ya cigaba da aiyukan alherin da ya faro.

Zaben 2019: Kawai ka manta da batun a sake zabenka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo

Amma sai dai waccan aniya da shugaba Buharin ya dauka ta tayar da kura a farfajiyar siyasar Najeriya, inda mutane da yawa suke sukar aniyar tasa, sakamakon gazawa da suka ce yayi wajen cika al’kawurran da ya dauka kafin a zabe shi.

A wata hira da Ghali Umar Na’abba yayi da Jaridar The Sun, ya bayyana cewa shi ya kasa gane menene ya bawa Buhari kwarin gwuiwar yunkurin sake tsayawa takara a 2019.

Na’abba yace a shawarce, kamata yayi Buhar ya sake tunanin sake tsayawa takarar da yace zai yi domin “Duk da cewa basu yi mamaki ba amma sun san bazai iya ba”.

Sirrin fararen Hakora: Hanyoyi 8 da za ku bi domin sanya Hakoranku suna sheki

“Tabbas abu ne mai sauki, tunda shi ne shugaba mai cikakken iko, yayi amfani da karfin mulkinsa, amma dai bisa la’akari da yadda abubuwa suke tafiya a haka, lallai ba kowa ne zai goyi da bayansa ba”. A cewa Alhaji Ghali.

Da yake amsa tambaya kan maganar da Obasanjo yayi na cewa, PDP da APC basu da cancantar da zasu iya gyara Najeria, Alhaji Na’abba cewa yayi, “ Kwarai na goyi da bayansa amma kuma shin a yadda ake tafiya yanzu, kana jin shugabannin da suke kai zasu iya barin wani ya gaje su bayan kuma sunyi karfi a kan mulkin sosai”?

Zaben 2019: Kawai ka manta da batun a sake zabenka

Zaben 2019: Kawai ka manta da batun a sake zabenka

Yan Najeriya Mutane ne masu wahalar karbar sauyi, amma kuma fa a yanzu muna cikin wani babban kalubale wanda na tabbata zasu nutsu su zabi gwamnatin da zata taimakesu fita daga cikin wannan halin, domin cika musu burinsu. Ni ina ji a zuciya ta komai na iya faruwa a 2019 na zabar sabuwar gwamnati.

"Tsora na kawai shi ne kar mu samu shugaban da zai zamo maras daukar shawara, iya rarrabuwar kan da muke da su a yanzu a kasar nan ya ishe mu, ba mu son kara wani, bin kullum kara rincabewa yake musamman yanzu. Don haka muna son wanda zai iya maganin wannan matsalar a kasar nan”. Kakakin Majalisar ya jaddada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel