Shugaba Buhari ya bayyana mutanen da suka jefa 'ya Najeriya cikin talauci

Shugaba Buhari ya bayyana mutanen da suka jefa 'ya Najeriya cikin talauci

Shugaba Buhari ya zargi wasu mutane da ya kira "mugwaye" da jefa Najeriya cikin kangin talauci da fatara.

Buhari ya furta haka ne yau a Landan yayin karbar bakuncin magoya bayansa dake kasashen ketare karkashin jagorancin Mista Charles Sylvester.

Shugaba Buhari ya kara da cewa gwamnatinsa tayi rawar gani ta fuskar farfado da tattalin arzikin Najeriya da kuma yakar fatara da talauci musamman idan aka yi la'akari da halin da tattalin arzikin kasa ke ciki lokacin da ya karbi mulki.

Shugaba Buhari ya bayyana mutanen da suka jefa 'ya Najeriya cikin talauci

Shugaba Buhari da magoya bayansa na kasashen ketare

Shugaban kasar ya ce ba kankanuwar illa gwamnatin baya ta yiwa tattalin arzikin Najeriya tare da shaidawa magoya bayan nasa cewar a halin yanzu tattalin arzikin Najeriya ya fara dawowa hayyacinsa.

Buhari ya jinjinawa kungiyar magoya bayansa dake kasashen ketare bisa hakurinsu da kokarin da suke yi wajen wayar da kan jama'a a kan irin kokarin gwamnatin APC keyi na sake gina Najeriya.

DUBA WANNAN: Hotunan shagalin bikin dan Atiku da aka yi a kasar Dubai

Da yake nasa jawabin, shugaban kungiyar, Sylvester, ya ce sun yi matukar farinciki da irin namijin kokari da shugaba Buhari ke yi musamman ta fuskar kirkirar hanyoyin rage radadin fatara da talauci ta hanyar shirye-shirye da dama da suka hada da N-POWER.

Kazalika ya jinjinawa kokarin Buhari a bangaren tsaro da kuma yadda gwamnati ta gaggauta kubutar da 'yan matan Dapchi da aka sace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel