Jam’iyyar APC ta bude sababbin shafukan sadarwa bayan an yi mata kutse

Jam’iyyar APC ta bude sababbin shafukan sadarwa bayan an yi mata kutse

- Jam’iyyar APC a Najeriya ta bude wasu sababbin shafukan sada zumunta dazu

- A jiya ne aka yi wa shafin da aka san Jam’iyyar mai mulki a kasar da shi kutse

- APC tace ta bude sabon shafin yanar gizo da na sada bayanai na zamani yanzu

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sanar da cewa ta bude sababbin kafofin sadarwa na zamani bayan da aka wayi gari aka ji cewa shafin Jam’iyyar ya fada hannun wani mutumin kasar waje da yanzu yake talla da shafin a Tuwita.

Jam’iyyar APC ta bude sababbin shafukan sadarwa bayan an yi mata kutse

APC ta bude sababbin kafofin sadarwa na zamani

Jam’iyyar APC ta bude sababbin kafofin sadarwa na zamani ne inji Sakataren yada labaran ta watau Bolaji Abdullahi domin nesanta kan ta daga tsohon shafin da ya shahara da sunan ta. APC dai tace ba ta san da zaman shafin APCNigeria ba.

KU KARANTA: Shafin APC ya fada hannun wani mutumi 'dan kasar waje

Shafukan da Jam’iyyar APC ta bude dai a yau dinnan su ne https://www.instagram.com/officialapcng (Instagram) da kuma https://web.facebook.com/officialapcng (Facebook) sai kuma https://twitter.com/OfficialAPCNg (Tuwita).

Bayan nan kuma an bude shafin yanar gizo www.officialapcng.com wanda za a rika sanar da jama’a al’amurran Jam’iyya a fadin kasar da kuma Jihohin da ta ke mulki a kai-a kai inji Sakataren yada labarai Bolaji Abdullahi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel