Za mu tabbatar da Gwamna Fayose ya je gidan yari - Ministan Buhari

Za mu tabbatar da Gwamna Fayose ya je gidan yari - Ministan Buhari

Babban ministan harkokin ma'adinai kuma daya daga cikin 'yan gaban goshin gwamnatin shugaba Buhari Mista Kayode Fayemi ya bayyana cewa jam'iyyar sa ta All Progressives Congress (APC) za ta tabbatar da cewa Gwamnan jihar Ekiti na yanzu ya je gidan yari da zarar ya sauka daga mulki.

Mista Fayeme kamar yadda muka samu yayi wannan ikirarin ne a lokacin da yake jawabi ga dumbin magoya bayan sa ranar Asabar din da ta gabata yayin taron gangamin sa na neman sake zama gwamnan jihar.

Za mu tabbatar da Gwamna Fayose ya je gidan yari - Ministan Buhari

Za mu tabbatar da Gwamna Fayose ya je gidan yari - Ministan Buhari

KU KARANTA: Buhari bai da nagartar neman tazarce - Na'abba

Legit.ng dai ta samu cewa a wajen taron, Ministan na Buhari ya kara da cewa akwai ayyuka da dama da ya fara a jihar amma aka murde masa zabe aka hana shi ya karasa su shine ma dalilin da yasa ke son ya sake tsayawa takarar gwamnan jihar.

A wani labarin kuma, Tsohon kakakin majalisar wakillai ta Najeriya kuma dan asalin jihar Kano Alhaji Ghali Umar Na'abba ya bayyana cewa shi dai bai ga da wane ido shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai kalli 'yan Najeriya ba har ya ce su sake zabar sa a 2019.

Tsohon kakakin majalisar dai ya ayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da kamfanin jaridar Sun inda ya bayyana takaicin sa ga wadanda yace sun karfafawa shugaban kasar gwiwa don ya sake tsayawa takarar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel