'Yan matan Chibok: Fadar shugaban kasa ta karyata Ahmed Salkida

'Yan matan Chibok: Fadar shugaban kasa ta karyata Ahmed Salkida

Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi kakkausar suka zuwa ga fitaccen dan jaridar nan da ake kyautata zaton yana da alaka mai karfi da kungiyar 'yan ta'addan nan ta Boko Haram mai suna Ahmed Salkida game da ikirarin da yayi na cewa yanzu 'yan matan Chibok 15 ne kacal ke da rai.

Fadar shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun babban mai taimakawa shugaban kasar a harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya bayyana cewa a gwamnatance wannan labarin kanzon kurege ne kawai.

'Yan matan Chibok: Fadar shugaban kasa ta karyata Ahmed Salkida

'Yan matan Chibok: Fadar shugaban kasa ta karyata Ahmed Salkida

KU KARANTA: Mutum 3 da ka iya kawo wa Buhari cikas a 2019 cikin APC

Legit.ng ta samu cewa ya kuma tabbatar wa 'yan Najeriya musamman ma iyayen yaran da su sani cewa dukkan bayanan da ke a hannun gwamnati na nuni ne da cewa 'yan matan sunanan da ran su.

A wani labarin kuma, Rundunar dakarun sojojin Najeriya a jiya ta bayar da labarin samun nasarar da suka yi na fatattakar wasu 'yan Boko Haram tare da kashe bakwai daga cikin mayakan su a wani gumurzu da akayi a cikin dazukan jihar Borno.

Kanal Onyema Nwachukwu dake zaman mataimakin daraktan dundunar tabbatar da zaman lafiya dake yaki da 'yan ta'addan ne dai ya sanar da hakan ga manema labarai a can garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel