Yadda jigo a APC ya sa aka yi waje da Shugaban Jam’iyya John Odigie-Oyegun

Yadda jigo a APC ya sa aka yi waje da Shugaban Jam’iyya John Odigie-Oyegun

- Bola Tinubu yana cikin wadanda su ka hana a karawa Oyegun wa’adi

- Wani babba a Jam’iyyar yace hakan kuwa ya taimakawa APC matuka

- Kwamitin Tinubu ya kuma hana a daura Shugabannin je-ka-na-yi-ka

Wani babba a Jam’iyyar APC a Kasar Kudu maso gabashin Najeroua Hyacinth Ngwu ya bayyana cewa Bola Tinubu yayi namijin kokari waje ganin cewa rikici bai kaure a Jam’iyyar ta APC mai mulki ba na dakatar da John Oyegun.

Yadda jigo a APC ya sa aka yi waje da Shugaban Jam’iyya John Odigie-Oyegun

Tinubu ya ceci APC daga zama irin PDP inji Huth

Idan ba ku manta ba, Jam’iyyar APC tayi yunkurin kara wa’adin Shugaban ta na kasa John Oyegun. Hyacinth Ngwu ya bayyanawa Jaridar Punch cewa Bola Tinubu yayi kokari wajen ganin wannan kama-karya ba ta zauna ba.

KU KARANTA: APC ta ba Shugaban kasa wuka da nama a takara mai zuwa

Kwanakin baya ne Shugaba Buhari ya nada Jigon na APC Bola Tinubu da ya dinke barakar Jam’iyyar. Daga cikin abubuwan da Kwamitin tayi a APC shi ne dakatar da yunkurin karawa Shugabannin ta wa’adi ta bayan fage.

Hyacinth Ngwu wanda yana cikin manyan Jam’iyyar yace kwamitin na Tinubu ya cin ma ayyukan da ke gaban sa. Bola Tinubu ya kuma nuna cewa babu dalilin kafa wasu Shugabannin rikon kwaya a APC sai dai kurum ayi sabon zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel