Jita-jitar jingine Osinbajo: APC ta bawa Buhari wuka da nama

Jita-jitar jingine Osinbajo: APC ta bawa Buhari wuka da nama

Jam'iyyar APC mai mulki ta ce ba zata yi kokarin kakabawa shugaba Buhari abokin takara a zaben 2019 ba idan ya yi nasarar samun tikitin takara.

Kazalika jam'iyyar ta APC ta ce ba zata matsawa shugaba Buhari daukar mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, a matsayin abokin takarar sa ba.

Sai dai a yayin da ya bayyana niyyar sa ta sake tsayawa takara a ranar Litinin da ta gabata, Buhari, bai ambaci da waye zai sake yin takara a matsayin mataimaki ba.

Jita-jitar jingine Osinbajo: APC ta bawa Buhari wuka da nama

Buhari da Osinbajo

Kazalika bai nuna wata alama dake nuna zai jingine mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ba.

Sakataren yada labaran jam'iyyar APC, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce ba zasu yi kokarin yin nune ko zabawa Buhari mataimaki ba.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Majalisar wakilai ta aikewa Osinbajo sammaci, zata yi masa titsiya a kan wani mataki da ya dauka

Wasu kusoshi a cikin jam'iyyar APC da tun a shekarar 2015 basu so yadda Tinubu ya yi uwa ya yi makarbiya a batun tsayar da Osinbajo tare da Buhari ba, na kokarin ganin a wannan karo sun danne karfin Tinubu ta hayar canja Osinbajo a matsayin abokin takarar Buhari a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel