2019: Zabe na karatowa PDP na kara rugujewa a yammacin Najeriya

2019: Zabe na karatowa PDP na kara rugujewa a yammacin Najeriya

- Jam'iyyar PDP ta shiga rudani a yammacin Najeriya

- wasu manyan kusoshin jam'iyyar na gab da ficewa

Watanni goma gabannin zaɓen 2019, da kuma wasu zaɓuka biyu na gwamnoni da za'a yi a ƙasashen kudu maso yammacin Najeriya a jahohin Osun da Ekiti, yanzu haka jam'iyyar PDP na shirin shiga cikin sabon ruɗani sakamakon raɗeraɗin aniyar ficewa da wasu uku daga cikin jiga-jigan jam'iyyar a yankin.

2019: Zabe na karatowa PDP na kara rugujewa a yammacin Najeriya

2019: Zabe na karatowa PDP na kara rugujewa a yammacin Najeriya

Jaridar Tribune ta rawaito cewa, tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Rashidi Ladoja da tsohon gwamnan Ondo, Dr Olusegun Mimiko da kuma mataimakin gwamnan kuma dan takarar PDP a 2014 a Osun Sanata Iyiola Omisore suna gab da ficewa daga jam'iyyar ta PDP.

An rawaito cewa dai, jiga-jigan jam'iyyar su ukun sunyi wani taro tsakaninsu domin tattauna irin matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta a yankin tun bayan da Shugabannin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Uche Secondus su kayi yunkurin dinke ɓarakar jam'iyyar a shiyyar.

shugabannin dai su uku, sun cimma matsayar cewa, ficewa daga jam'iyyar shi ne mafita, amma sai dai suna tararrabin komawa wata sabuwar jam'iyyar. Wasu rahotanni sun nuna cewa, yanzu haka wasu suna can suna tattaunawa da shuwagabannin wasu jamiyyun da suke shinshinawa domin komawa.

KU KARANTA: Kudin makamai: Jihar Bayelsa ta yi barazanar maka gwamnatin Buhari kotu

Ana zaton dai Ladoja da magoya bayansa zasu iya komawa jam'iyyar Alliance for Democracy (AD). Shi kuma Omosire da nasa magoya bayan na tattaunawa da jam'iyyar SDP, shi kuma Mimiko na shirin kowa jam'iyyar da yaci zaɓe a cikinta har sau biyu wato Labour Party (LP).

Wata majiya ta bayyana cewa, an kafa wani kwamiti da zai tattauna da Shugabannin jam'iyyar AD, a wani zama da aka gudanar a gidan Lodoja ranar Laraba domin ficewa daga jam'iyyar ta PDP a sakamakon rashin adalcin da suka ce anayi musu. Kamar yadda Tribune ta rawaito.

An dai rawaito cewa, wannan shawara da suka yanke na da nasaba da ƙorafin da wasu gungun magoya bayan wani ɗan takarar gwamna a jihar, wanda hakan bai yiwa Shugabannin jam'iyyar daɗi ba, a saboda haka ƴan takarar gwamna suka nemi Lodoja da ya sanya baki a cikin maganar.

Bayanai sun nuna cewa Osi Olubadan, ya sami Shugaban jam'iyyar Secondus domin shigar da wancan korafi a makwanni biyu da suka shuɗe.

2019: Zabe na karatowa PDP na kara rugujewa a yammacin Najeriya

2019: Zabe na karatowa PDP na kara rugujewa a yammacin Najeriya

Sai dai Shugaban Jam'iyyar wanda yayi alƙawarin daukar mataki kan batun yayi tsit bai ce komai ba yayin taron da aka yi a gidan Sanata Ben Obi, bayan yayi alƙawarin ɗaukar mataki.

Yayinda a jihar Osun kuwa, baya ce ta haihu, inda bayan kammala taron jam'iyyar PDP da aka gudanar da sunan sulhu ga gida-gidan jam'iyyar na jihar ne ya ƙara taɓarɓarewa.

Su kuwa shuhada'un Omisore, bayanai sun nuna cewa wariyar launin fata akai musu daga cikin waɗanda zasu jagoranci ragamar jam'iyyar a jihar.

Jam'iyyar PDP dai ita ce babbar jam'iyyar adawa da APC mai mulki, kuma PDP tayi alkawarin dawowa ta sake karbe ragamar shugabancin kasar nan tun bayan da ludayinta ya subuce daga kan dawo, amma kuma in dai irin haka ta cigaba da faruwa, rikicin yau daban na gobe daban a PDP to za'a iya cewa basu shirya karɓar mulki daga hannun APC ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel