Kwamacala: An saidawa wani farar fata Jam’iyyar APC a kan kudi $2000

Kwamacala: An saidawa wani farar fata Jam’iyyar APC a kan kudi $2000

A jiya ne wani mutumin kasar waje mai suna Justine Sun ya saye shafin Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya na sada zumunta na Tuwita ya kuma ce idan da hali kuma yana nema a saida masa kasar. Sai da alama akwai wata maganar.

Kwatsam jiya sai aka ji cewa shafin APC ya koma na wani mutumi wai shi Mista Sun inda ya tabbatar da cewa Shugaban kasar ne ya saida masa shafin Jam’iyyar mai mulki har kuma aka yi masa tayin wasu shafukan kasar dabam.

Kwamacala: An saidawa wani farar fata Jam’iyyar APC a kan kudi $2000

Wani yayi ikirarin sayen shafin Tuwita na APC a Najeriya

Jiya ne Justin Sun ya bayyana cewa ya saye shafin ne wanda ke da masoya sama da 700, 000 a kan kudi Dala 2000. Idan dai aka juya wannan kudi a Najeriya zai tashi a kan N700, 000 kenan wanda yace ya ji dadin wannnan cinikin ainun.

KU KARANTA: An nemi APC ta tsaida Kwankwaso takara a 2019

Kwamacala: An saidawa wani farar fata Jam’iyyar APC a kan kudi $2000

Wasu na ganin kutse wannan mutumi yayi wa shafin na APC

Sai dai kuma Sun yayi barazanar cewa idan ba a ba shi Dala 100, 000 ba (watau Miliyan 35) zai fallasa duk wani sirri da aka yi ta shafin saboda kuwa ba a rasa tattaunawar da aka yi tsakanin Jam’iyyar mai mulki da Hukumomin kasar.

Wannan mutumi yace idan aka yi masa tayin Najeriyar ma a shirya yake da ya saya. Ita kuwa APC ta tubure tace ita ba ta san da zaman wannan shafin na @APCNigeria ba duk da cewa da sunan ta ake aiki da shi tun tuni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel