Wani Masaki ya fyade 'yan mata 4 a jihar Kebbi

Wani Masaki ya fyade 'yan mata 4 a jihar Kebbi

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, mazauna yankin garin Badariya dake Birnin-Kebbi a jihar Kebbi sun cika da mamaki yayin da aka damke wani masaki Abdulazeez Jega mai shekaru 30 da ya saba yin lalata da wasu matasan mata hudu a yankin.

Kungiyar tsaro ta 'yan bijilanti ce ta damko wannan gurgu da ya saba yin lalata da 'yan matan a shagon sa dake yankin.

A yayin gabatar da wannan mugun gurgu ga manema labarai, shugaban kungiyar Alhaji Lawal Augie ya bayyana cewa, mazauni yankin na Badariya ne ke da alhakin damke shi yayin da yake tsaka da lalata.

Wani Masaki ya fyade 'yan mata 4 a jihar Kebbi

Wani Masaki ya fyade 'yan mata 4 a jihar Kebbi

Rahotanni sun bayyana cewa, kungiyar ta yi nasarar cafke masakin ne yayin da mai garin Badariya ya karbi korafin al'ummar sa da cewa wani shu'umin mutum yana lalata da 'yan matan su a yayin da suke yawan tallace-tallace.

Legit.ng ta fahimci cewa, makamancin wannan mugun hali na gurgun ya sanya aka fatattake shi daga wurin zaman sa dake karamar hukumar Jega ta jihar Kebbi.

KARANTA KUMA: Mutane 3 sun mutu yayin da cutar kwalara ta addabi al'ummar jihar Borno

A halin yanzu dai an mika shi ga hukumar Hisbah domin daukar matakin da ya dace kasancewar ta hukumar kiyaye ladubba na al'adu da kuma addini.

A yayin tuntubar 'yan matan da gurgun ya saba yiwa aika-aika, sun tabbatar da cewa ya kan yaudare su da abin duniya inda su kuma kwadayi ke sanya wa su afkawa tarkon sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel