Gwiwar mu ba zata taba yin sanyi ba, martanin hukumar soji kan mutuwar 'yan matan Chibok

Gwiwar mu ba zata taba yin sanyi ba, martanin hukumar soji kan mutuwar 'yan matan Chibok

- Hukumar tsaro na Najeriya ta mayar da martani akan rahoton cewa yan matan Chibok 15 ne kawai ke raye a yanzu

- Hukumar tace ba yau aka saba fadin irin wannan maganganun ba kuma gwamnati ba zata karaya ba wajen cigaba da kokarin ceto yan matan

- Rahoton dai ya fito ne bakin sananen dan jarida mai kawo rahoto daga kungiyar ta Boko Haram, Ahmed Salkida

Kakakin hukumar tsaro na kasa, John Agim ya mayar da martani kan rahoton da wani dan jarida, Ahmed Salkida ya bayar inda yace yan matan Chibok 15 ne kawai suka a raye cikin 113 da aka sace inda yace gwamnatin na kan bakanta na ceto yan matan kuma zancen ba zai gwamnati ta karaya ba.

Ahmad Salkida dai sananen dan jarida ne wanda ya saba samo rahoto daga shugabanin kubgiyar Boko Haram yace galibin yan matan sun mutu a sansanin na yan Boko Haram. Ya kuma ce sauran da ke raye duk an aurar da su.

Gwiwar mu ba zata taba yin sanyi ba, martanin hukumar soji kan mutuwar 'yan matan Chibok

Gwiwar mu ba zata taba yin sanyi ba, martanin hukumar soji kan mutuwar 'yan matan Chibok

DUBA WANNAN: 'Yan Shi'a sun raba ruwan gora a maulidin 'yan darika a Abuja

Salkida ya kallubalanci gwamnati ta fadawa al'umma gaskiya ta dena kumbiya-kumbiya akan zancen.

"Ina mai juyayin fadawa al'umma cewa cikin yan matan Chibok 133, guda 15 kawai ke raye a yanzu kamar yadda binciken da nayi cikin watanni uku suka nuna," kamar yadda Salkida ya rubuta a Twitter.

Salkida ya kuma kara da cewa ya shafe shekaru 13 yana bincike da kuma dauko rahoto akan ayyukan ta'addancin da ke faruwa a yankin na arewa maso gabashin Najeriya saboda haka babu wanda zai ce bashi da masaniya akan abubuwan da ke faruwa a yankin.

Sai dai a yayin da Agim ya ke amsa tambayoyi da jaridar The Cable tayi masa, yace wannan ba shine karo na farko da ake cewa an aurar da yan matan ba amma duk da haka gwamnati bata karaya ba kuma gashi an ceto wasu daga cikin yaran.

"Kawai suna son gwamnati ta karaya ne," inji Agim.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel