2019: Mutane 10 da shugaba Buhari ya dogara da su domin samun tazarce

2019: Mutane 10 da shugaba Buhari ya dogara da su domin samun tazarce

A ranar Litinin 9 ga watan Afrilu, shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin jawaban sa a yayin taron shugabannin jam'iyyar su ta APC ya bayyana kudirin sa na sake neman takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 a karo na biyu.

2019: Mutane 10 da shugaba Buhari ya dogara da su domin samun tazarce

2019: Mutane 10 da shugaba Buhari ya dogara da su domin samun tazarce

Wannan kudiri na shugaba Buhari na cin karo da ra'ayoyin wasu jiga-jigai a kasar nan irin su tsaffin shugabanni Olusegun Obasanjo, Ibrahim Babangida da kuma Janar TY Danjuma kamar yadda ya sha suka ban-ban da kudirin tsohon shugaba Goodluck Jonathan na sake neman takara.

Legit.ng da sanadin hasashe da kuma bincike na jaridar Daily Trust ta kawo muku jerin sunayen wasu jiga-jigan kasar nan da shugaba Buhari zai dogara da su domin samun nasara ta cimma manufar sa.

KARANTA KUMA: Bincike: Ababe 8 da Maza ke la'akari da su yayin lura da Mata

Binciken ya bayyana cewa, wannan mutane za su taka muhimmiyar rawa a yankunan su wajen baiwa shugaba Buhari dama ta yin tazarce a zaben 2019 mai gabatowa.

Wannan mutane na da muhimman da karfin gaske a yankunan su ta fuskar siyasa wanda ake sa ran taimakon su zai tabbatar da nasarar shugaba Buhari ta yin tazarce.

Jiga-jigan kasar nan da zau tabukawa Buhari wajen tabbatar da nasarar sun hadar da:

1. Tsohon gwamnan jihar Legas; Bola Tinubu

2. Shugaban majalisar dattawa; Bukola Saraki

3. Tsohon gwamnan jihar Kano; Sanata Rabiu Kwankwaso

4. Uwargidan shugaban kasa; Aisha Buhari

5. Gwamnan jihar Sakkwato; Aminu Waziri Tambuwal

6. Gwamnan jihar Ebonyi; Dave Umahi

7. Kakakin majalisa; Yakubu Dogara

8. Shugaban jam'iyyar APC na jihar Bayelsa; Timipre Sylva

9. Tsohon gwamnan jihar Gombe; Sanata Muhammad Danjuma Goje

10. Majalisar yakin neman kujerar shugaban kasa ta jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel