Mutum 3 da ka iya kawo wa Buhari tsaiko a batun takarar sa ta tazarce a jam'iyyar APC

Mutum 3 da ka iya kawo wa Buhari tsaiko a batun takarar sa ta tazarce a jam'iyyar APC

Biyo bayan ayyana kudurin sake tsayawa takarar tazarce da shugaba Muhammadu Buhari yayi a satin da ya gabata yayin taron masu ruwa-da-tsaki na jam'iyyar APC mai mulki, alamu na ta nuna yiwuwar ficewar wasu jiga-jigan jam'iyyar zuwa wasu jam'iyyun domin samun tikitin takara a 2019.

Mutum 3 da ka iya kawo wa Buhari tsaiko a batun takarar sa ta tazarce a jam'iyyar APC

Mutum 3 da ka iya kawo wa Buhari tsaiko a batun takarar sa ta tazarce a jam'iyyar APC

KU KARANTA: Jiga-jigan jam'iyyar APC na shirin ficewa

Duk da dai har yanzu ba'a fallasa sunayen masu neman ficewa daga jam'iyyar ba, amma dai jam'iyyun da ake tunanin za su yi sabbin baki sun hada da Social Democratic Party (SDP), Labour Party (LP), Accord Party (AP) da kuma hadakar nan ta tsohon shugaba Obasanjo ta Coalition for Nigeria Movement (CNM).

To sai dai, masana harkokin siyasa da masu sharhi akan al'amurran yau-da-kullun na kasar nan suna ganin cewa wasu za su iya tsayawa a cikin jam'iyyar domin neman takarar.

Wadanda ake tunanin za su iya tsayawa a jam'iyyar har kuma su iya kawo wa shugaba Buhari tsaiko din dai sun hada da:

1. Sanata Bukola Saraki

2. Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

3. Aminu Waziri Tambuwal

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel